Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

- Manema labarai sun sha da kyar a hannun fusatattun matasa a garin Jangabe na jihar Zamfara

- Lamarin ya afku ne lokacin da yan jaridar suka isa garin domin samo rahoto kan sace yan matan GGSS da yan bindiga suka yi

- Wani daga cikin yan jaridar da aka farma ya samu mummunan rauni inda aka garzaya da shi asibitin Gusau

‘Yan jarida suka tsallake rijiya da baya a Jangebe, garin Zamfara inda aka sace ‘yan mata kusan 500 a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu.

An kai wa 'yan jaridar hari ne lokacin da suka isa garin domin samun rahoto kan sace 'yan matan.

Fusatattun matasa sun afkawa motoci biyu da ke dauke da ‘yan jarida daga kafofin watsa labarai na Daily Trust, NAN, AIT, TVC, Channels da kuma wata kafar yada labarai ta yanar gizo Thunder Blowers wanda mai daukar hoton nasa ya ji mummunan rauni a goshinsa.

Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya
Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

A yanzu haka an garzaya da shi Gusau, babban birnin jihar don karbar magani.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

Matsalar ta fara ne lokacin da mazauna garin suka hango motocin da ke dauke da 'yan jaridar.

Sun fara jifan motocin da duwatsu da wasu abubuwa masu hadari inda wasu matasa suka ce a cinna musu wuta.

Sai da direbobin motocin da ke jigilar 'yan jaridar suka yi saurin dage gilashinsu inda aka fasa wasu bangarori na gilashin.

An tattaro cewa ayarin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a jihar ma sun sha jifa da duwatsu lokacin da ya ziyarci yankin.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Daga Chibok zuwa Jangebe, Dalibai 1,140 aka sace a cikin shekaru bakwai

An ga mazauna yankin, wadanda akasarinsu matasa ne dauke da sanduna, adduna da sauran muggan makamai.

Da yake maida martani game da lamarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Mista Abutu Yaro, ya yi kira da a kwantar da hankula, yana mai cewa nuna fushin ba zai taimaka ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sanda a Zamfara ta ce kimanin dalibai 317 aka sace daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta' Yan Mata ta Gwamnati da ke Jangebe, a jihar.

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun kai harin tsakar dare makarantar wanda ke a karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar.

Da yake martani a kan ci gaban, Kwamishinan 'yan sanda na Zamfara, CP Abutu Yaro ya ce tuni aka fara gudanar da aikin bincike tare da kokarin ceto dalibai 317 da maharan suka sace.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng