Ku gayyaci Gumi da Shekau kafin ku dame ni, Igboho ya magantu bayan dakile kamunsa

Ku gayyaci Gumi da Shekau kafin ku dame ni, Igboho ya magantu bayan dakile kamunsa

- Sunday Igboho ya aike da gargadi ga gwamnatin tarayya

- Dan gwagwarmayar Yarbawan ya fada wa gwamnati da ta fuskanci ‘yan fashi da masu tayar da kayar baya da ke addabar kasar

- Igboho ya yi artabu mai zafi da hadaddiyar tawagar DSS da ‘yan sandan Najeriya a ranar Juma’a

Sunday Adeyemo, wani dan gwagwarmayar Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya fada wa gwamnatin tarayya da ta cire shi daga cikin jerin gwanon da take yi sannan ta bi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da 'yan fashi.

Igboho ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a 26 ga Fabrairu, bayan da aka dakile kama shi da jami’an tsaro suka yi yunkurin yi.

KU KARANTA KUMA: An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane

Legit.ng ta rahoto a baya cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun tsare motar dan fafutukan a hanyar babban titin Lagas-Ibadan.

An tattaro cewa dan fafutukan Yarbawan na kan "hanyarsa ta ganin Baba Ayo Adebanjo", wani dattijo yarbawa kuma daya daga cikin shugabannin Afenifere a Legas.

Igboho wanda ya yi magana a wani faifan bidiyo wanda yanzu ya fara yaduwa ya ce ya koma gidansa da ke Ibadan.

“Ku je ku sa su gayyato Gumi da Shekau tukuna kafin su dame ni. A bar su su fuskanci ‘yan fashin maimakon haka,” kamar yadda ya fada wa jaridar The Punch bayan artabun da suka yi da jami’an tsaro.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda

A wani labarin, wani tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Dokta Obadiah Mailafia, ya ce da yawa daga cikin ‘yan fashin da ke addabar kasar nan wasu mutane ne suka dauki nauyin su da ke son su ture tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga mulki ta kowane hali.

Mailafia ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Punch a ranar Alhamis.

Ya ce, “A lokacin zaben 2015 sun shigo da dubban 'yan kasashen ketare cikin kasar nan, suna ba su makamai saboda lamari ne na idan Goodluck Jonathan bai mika wuya ba, za a yi yaki. Sun kasance a shirye don yakin basasa; ba su kasance a shirye don zaman lafiya ba."

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng