Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda

Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda

- Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa dalibai mata 317 yan bindiga suka sace daga GGSS Jangabe

- Sai dai kwamishinan yan sandan jihar, CP Abutu Yaro ya ce tuni rundunar hadin gwiwa ta yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka dukufa zuwa inda ake zaton an tafi da yaran

- Ya kuma yi kira ga iyaye a kan su kwantar da hankalinsu domin za a kai ga nasara

Rundunar yan sanda a Zamfara ta ce kimanin dalibai 317 aka sace daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta' Yan Mata ta Gwamnati da ke Jangebe, a jihar.

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun kai harin tsakar dare makarantar wanda ke a karamar hukumar Talata-Mafara ta jihar.

Da yake martani a kan ci gaban, Kwamishinan 'yan sanda na Zamfara, CP Abutu Yaro ya ce tuni aka fara gudanar da aikin bincike tare da kokarin ceto dalibai 317 da maharan suka sace, Channels TV ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda
Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Daga Chibok zuwa Jangebe, Dalibai 1,140 aka sace a cikin shekaru bakwai

CP Yaro ya ce kwamandan rundunar Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Aminu Bande, Birgediya kwamanda na Brigade 1, Sojojin Najeriya Gusau, da sauran jami’an gwamnatin jihar sun jagoranci wata tawaga mai dauke da kayan aiki zuwa Jangebe.

Sun yi wannan jagoranci ne don taimakawa a aikin ceto da ke gudana a wuraren da ake zaton nan aka kai daliban.

Kwamishinan yayin ganawa da Shugaban makarantar da iyaye, ya yi kira ga kowa da ya kwantar da hankali saboda kokarin da hadin gwiwar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zai cimma nasara wajen ceto daliban.

KU KARANTA KUMA: Zan dafa wa mijina abinci sau uku a rana, wata budurwa ta sanar da mata masu tsatsauran ra’ayi

A gefe guda, Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace daliban makarantar sakandare na mata a Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara da ke jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran ne ya tabbatar da hakan a cikin wata hira da Kamfanin dillancin labaran Najeriya a Gusau, a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu.

Daruruwan masu garkuwa da mutanen sun kai mamaya garin sannan suka tafi da yaran da misalin karfe 2:00am.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel