Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

- Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace daliban GGSS Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara

- Daruruwan maharan sun kai farmaki yankin ne da karfe 2:00 na tsakar daren ranar Juma'a

- Zuwa yanzu ba a san yawan daliban da yan bindigan suka sace ba

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace daliban makarantar sakandare na mata a Jangebe da ke karamar hukumar Talata-Mafara da ke jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Dauran ne ya tabbatar da hakan a cikin wata hira da Kamfanin dillancin labaran Najeriya a Gusau, a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu.

Daruruwan masu garkuwa da mutanen sun kai mamaya garin sannan suka tafi da yaran da misalin karfe 2:00am.

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi
Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi Hoto: BBC
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

“Zan iya tabbatar maku yanzu cewa mun samu rahoton bakin ciki na sace daliban GGSS Jangebe kuma a yanzu, Ina a hanyata ya zuwa makarantar.

“A wannan lokacin, ba zan iya cewa dalibai nawa yan bindigan suka sace ba har sai na kai wajen, amma tuni muka tura jami’an tsaro da yan banga domin su bi sahun masu garkuwan,” in ji kwamishinan.

Wani ma’aikacin makarantar wanda ya zanta da NAN bisa sharadin boye sunansa ya ce: “daruruwan yan bindigan sun kai mamaya garin da misalin karfe 2:00 an tsakar daren ran Juma’a, suna ta harbi ba kakkautawa a sama don tsorata mazauna yankin kafin suka shigo makarantar.

“Bayan sun tafi da yawancin daliban, sai muka hada wadanda suka tsere ko suka boye ma yan bindigar sannan muka kirga su inda muka kirga dalibai 54 kuma har yanzu muna duddubawa muga ko zamu samu karin wasu.”

KU KARANTA KUMA: Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya

Wani mazaunin yankin da ya bayar da sunansa a matsayin Haliru Jangebe ya ce, yan banga sun yi kokarin dakile harin amma aka sha karfinsu.

A baya mun kawo cewa yan bindiga sun sace daliban makaranta mata a jihar Zamfara.

Majiyoyin Legit Hausa sun tabbatar da ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata wanda ba'a san ainihin adadinsu ba har yanzu daga makarantar sakandiren GSS Jengebe, karamar hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara.

Majiyoyin sunce an sace wadannan dalibai ne misalin karfe daya na dare.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng