Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami

Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami

- Malamin makarantar Jangebe da aka sace yara yace iyayen yara sun ragargaza makarantar

- Kamar yadda ya bayyana, iyayen sun tsinkayi makarantar inda hukuma ta hana su shiga ciki

- Wasu iyayen sun dinga yanke jiki suna faduwa yayin da wasu suka dinga lalata tagogi da kofofi

Daya daga cikin malaman makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke Jangebe a jihar Zamfara ya bada labarain yadda wasu fusatattun iyaye suka balle tagogi da kofofin makarantar bayan sace yaransu da aka yi.

'Yan bindiga sun tsinkayi makarantar da sa'o'in farko na ranar Juma'a inda suka yi garkuwa da dalibai mata.

A yayin zantawa da Daily Trust, malamin yace iyayen yaran sun gaggauta zuwa makarantar bayan aukuwar lamarin.

KU KARANTA: Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami
Iyayen yara sun ragargaza makarantar da aka sace dalibai mata a Zamfara, Malami. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ce iyayen wasu daga cikin yaran da aka sace sun yanke jiki sun fadi a makarantar yayin da wasu da suka ga yaransu suka yi kokarin tafiya da su amma aka hana su.

Amma kuma iyayen sun dauka mataki inda suka kutsa cikin makarantar.

"Da farko hukumar makarantar ta hana su shiga cikin sauran daliban amma sun fusata inda suka dinga balle tagogi da kofofin gine-ginen makarantar," yace.

Malamin ya ce bayan kwashe daliban da aka yi, daliban da suke makarantar basu wuce 50 ba daga cikin wurin 600 da ke makarantar.

Ya ce 'yan bindigan sun fara da kaiwa sojoji farmkai a garin kafin su shiga makarantar.

KU KARANTA: Hotunan miyagun makaman da Zikwi tare da yaransa 2 suka mika ga Matawalle

A wani labari na daban, sojojin Najeriya sun datse farmakin da 'yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Boko Haram suka kaiwa fasinjoji a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Auno da ke jihar Borno.

Duk da sojin sun fatattaki 'yan ta'addan, majiyar sirri daga rundunar ta sanar da PRNigeria cewa an ceto fasinjoji masu tarin yawa da ke ababen hawa na haya a Auno.

Dakarun bataliya ta 212 da ke Jakana, Goni Masari da Auno sun gaggauta zuwa wurin sannan suka raka fasinjojin zuwa Damaturu da Maiduguri.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng