Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya

Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya

-Barkina Faso wacce ke fama da talauci da kuma ɗaya cikin ƙasahen da ke fama da ayyukan ta'addanci sun yi rawar gani.

-Rudunar sojin ƙasar ce dai ta kai wani hari inda ta kashe mayaƙa masu dama.

-Kuma ko da a nan Najeriya ma ana fama da irin wananna matsala ta masu iƙirarin Jihadi.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya.

Dakarun sojin Barkina Faso sun bayyana cewa sun kashe mutane sha ɗaya a yayin wata arangama a Arewacin ƙasar da masu iƙirarin Jihadi bayan sun kai hari.

An dai kai musu harin ta ƙasa ta sama a wani daji mai suna Bangao na yankunan Tasmakat da Fourkoussou da Bidy a gundumar Oudalan a 23 da 24 na watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Jirgin Sama da Ya Ɗauko Fasinjoji Ya Ɓace a Sararin Samaniya

KARANTA WANNAN: KWABID-19 ta yi ajalin rear admiral Aikhomu

Adadin ƴan ta'addan dai sha ɗaya ne, inda aka kama ɗaya sannan an tabbatar da babu soja ko ɗaya da ya mutu.

Dakarun dai sun ƙwace makamai da alburasai da ababen hawa da na sadarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya
Sojojin Burkina Faso sun kashe ƴan tada ƙayar baya goma sha ɗaya Source: Punch Nigeria
Asali: Twitter

Mai maganar ya cigaba da cewa, "an kai samamen ne sakamakon cigaba da damun sibiliyan da suke yi a yankin na Oudalan, inda aka kashe mutane da ba su ji ba ba su gani ba har tara kuma aka raunata wasu da dama a jerin motocin da ke kan hanyarsu ta zuwan garin na Oudalan a ranar 18 ga Fabarairu."

An kuma kashe mata biyu da wani bam da aka ɗana a yankin Yagha a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: cikin hotuna sabon shugaban hukumar EFCC ya kawai shugaba muhammadu buhari ziyara.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Barkina Faso na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya wacce kuma ke cigaba da fama da masu iƙirarin jihadi wanda ya samo tushe daga maƙwabciyarsu Mali a shekarar 2012 kuma har ya tsallako musu a shekarar 2015. Sama da mutane dubu ɗari da ɗari biyu ne suka mutu, inda kuma miliyoyi suka yi gudun hijira.

A wani labarin, Jaridar The Tribune ta rawaito an dai ba da tabbacin ne ga baƙi waɗanda ba ƴan asalin jihar ta Gombe ba waɗanda kuma tarzomar garin Billiri ta shafa, inda gwamnati ta tabbatar musu da ƙoƙarinta wajen kare dukiyyi da rayukannsu.

An buƙaci mazauna wannan yanki da su koma wuraren kasuwancinsu ba tare da wata fargaba ta cin zarafi ko firgitarwa ba, matuƙar dai sun cigaba da kasancewa masu bin doka da oda.

Wannan tabbaci dai na zuwa ne daga bakin gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, a yayin zaman sasantawa da shuwagabannin unguwannin bayan samun tarzomar da ta ɓarke a yayin zanga-zangar lumanar da matasa suka yi a ƙaramar hukumar Billiri a satin da ya gabata.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

Sunana Anas Dansalma kuma na karanta harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Ni marubuci ne kuma mafassari. `

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng