Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani tsohon gwamna

Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani tsohon gwamna

- Wata kotun jihar Imo ta bukaci kwace dukkan kadarorin da tsohon gwamna Rochas Okorocha ya tara yayin da yake mulki

- Alkalin kotun, Fred Njemanze ya bada umarnin kwace dukkan kadarorin kamar yadda lauyan gwamnatin jihar ya bukata

- Ana zargin tsohon gwamnan da tara kadarorin ne ba bisa ka'ida ba tun daga shekarar 2011 zuwa 2019

Wata babbar kotun jihar da ke zama a Owerri, babban birnin jihar Imo ta bada umarnin kwace dukkan kadarorin da ake zargin tsohon gwamna Rochas Okorocha ya mallaka ba ta halas ba yayin da yake kujerar gwamnan jihar daga 2011 zuwa 2019.

Mai shari'a Fred Njemanze ya bada umarnin bayan bukatar da babban lauyan Najeriya, Louis Alozie ya mika a madadin gwamnatin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Wasu kadarorin da aka lissafa sun hada da jami'ar Eastern Palm da ke Ogboko, otal din Royal Spring Palm, kwatas din malaman IBC wacce aka ce gidauniyar Rochas ta samu ba bisa ka'ida ba, kwatas din majistare da sauransu.

KU KARANTA: Fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani tsohon gwamna
Kotu ta bada umarnin kwace kadarorin wani tsohon gwamna. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta fadi dalilinta na tabbatar da Bawa a matsayin shugaban EFCC

A wani labari na daban, wasu gungun 'yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari inda suka kashe dan sanda mai mukamin sifeta daga saman bishiya tare da raunata wasu 'yan sandan uku.

An gano cewa an tura 'yan sandan ne domin baiwa matafiya da ke kan babbar hanyar Minna zuwa Suleja kariya. Amma sai aka kai musu farmaki a ranar Talata da yammaci a wurin Kaffinkoro.

An gano cewa 'yan sandan na tsaye ne inda suke sintiri a kan babbar hanyar lokacin da 'yan bindigan suka yi musu ruwan harsasai daga saman bishiya.

A take sifetan ya fadi matacce yayin da sauran ukun suka jigata, Vanguard ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel