Majalisar dattawa ta fadi dalilinta na tabbatar da Bawa a matsayin shugaban EFCC
- Majalisar dattawan Najeriya ta kare kanta a kan tabbatar da Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC
- Kamar Yadda Sanata Suleiman Kwari ya sanar, Bawa ya kare kansa a gaban majalisa kuma sun gamsu
- Kwari ya kara da cewa, cece-kuce akan taba kama Bawa da laifin rashawa duk labaran kanzon kurege ne
Majalisar dattawa ta kare kanta a kan hukuncin da ta yanke na tabbatar da sabon shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.
Tabbatar da Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC ya faru ne a ranar Laraba jim kadan bayan ya bayyana gaban majalisar dattawan kuma sun tantancesa.
Tabbatar da Bawa tazo ne a lokacin da ake ta zargi tare da cece-kuce a kan rahoton cewa an taba kama sabon shugaban EFCC da laifin rashawa, Channels TV ta ruwaito.
KU KARANTA: Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi
Amma a yayin zantawa da gidan talabijin na Channels, sa'o'i kadan bayan tabbatar da Bawa, shugaban kwamitin yaki da rashawa na majalisar, Suleiman Kwari ya ce ba a taba kama Bawa da laifin rashawa ba.
"An samu wasu zarge-zarge da aka kasa tabbatarwa. Ba a taba tuhumar matashin ba, ba a taba kama shi ba kuma ya zo gaban majalisar ya kare kansa," yace.
A yayin da aka tambaya ko kwamitin yayi bincike da farko kafin tabbatar da Bawa, dan majalisar ya jaddada cewa duk abubuwan da ake fadi a kan Bawa zargi ne kawai.
Yayin tabbatar da cewa Bawa ya musanta dukkan zargin, Sanata Kwari ya ce yadda ya tsaya gaban majalisar ya gamsar da su, hakan yasa suka tabbatar da shi
KU KARANTA: Hotunan kyakyawar likita da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce nan babu dadewa za ta fara shari'ar wasu mutum 5,000 da ake zargi da zama 'yan ta'addan Boko Haram kuma suna tsare a gidajen gyaran halin kasar nan.
Darakta janar na kungiyar shari'a, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Borno, Babagana Zulum a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
Abubakar ya bayyana barikin Giwa da ke Maiduguri, gidan gyaran hali na Kainji a matsayin wuraren da aka adana wadanda ake zargin da ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng