Sulhu da yan bindiga ba shi bane mafita, Janar AbdusSalam ga Gwamnoni

Sulhu da yan bindiga ba shi bane mafita, Janar AbdusSalam ga Gwamnoni

Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soja, Janar Abdulasalmi Abubakar, ya ce sulhu da tsagerun yan bindiga ba shi bane mafita daga cikin halin da ake ciki ba.

Janar AbdusSalam ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin Najeriya, yayinda suka kai msa ziyara gidansa dake Minna, jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar tayi duk mai yiwuwa domin ceto daliban makarantar GSC Kagara.

"Sulhu da yan bindiga ba shi bane mafita amma idan mutum ke mulki, yaya zai yi? An sace yaranmu na tsawon kwanaki biyar yanzy, ko da ka san idan suka, ba zai yiwu ka shiga wajen da yaki ba saboda da yiwuwan a kashe yaran," AbdusSalam yace.

"Wani lokacin akwai bukatar nemo hanyar tattaunawa da wadannan mahaukatan domin su sake mutane. Amma sulhu da su ba shi bane mafita."

"Ya kamara hukumomin tsaro su hada karfi da karfe domin samar da sabuwar hanyar magance matsalar."

Sulhu da yan bindiga ba shi bane mafita, Janar AbdusSalam ga Gwamnoni
Sulhu da yan bindiga ba shi bane mafita, Janar AbdusSalam ga Gwamnoni
Asali: UGC

Gwamna Kayode Fayemi, wanda shine shugaban kungiyar kuma ya jagorancin tawagar gwamnonin ya yi alhinin satar dalibai makarantar Kagara.

Bayan ziyarar da suka kaiwa Abdus Salam, gwamnonin sun garzaya gidan tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida.

Makon daliban Kagara daya yanzu a hannun yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel