Alheri ne ga 'yan Najeriya hana kasuwancin Bitcoin, in ji gwamnan CBN

Alheri ne ga 'yan Najeriya hana kasuwancin Bitcoin, in ji gwamnan CBN

- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana alherin dake cikin hana kasuwancin Bitcoin

- Bankin yace alherine ga 'yan Najeriya da kuma kokarin karesu daga fadawa hatsarin sata

- Hakazalika gwamnan babban bankin ya bayyana shirin CBN kan tabbatar da dokar hanin

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ce shawarar bankin ta hana sanya bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi daga tallafawa cinikayyar kudaden intanet ya fi dacewa da ‘yan Nijeriya, P.M News ta ruwaito.

Gwamnan na CBN ya fadi haka ne a lokacin da yake yi wa kwamitin hadin gwiwar Majalisar Dattawa bayani game da harkar Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi kan umarnin hana hulda da kudaden intanet.

Emefiele wanda ya bayyana kudin intanet a matsayin mai hatsari ya ce amfani da shi ta wasu bangarori da dama ya saba wa dokar da ke akwai kuma ya saba wa dokar CBN da ta 2007.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta shiga zaman tantance sabon shugaban EFCC, Rasheed Bawa a yau

Alheri ne ga 'yan Najeriya hana kasuwancin Bitcoin, in ji gwamnan CBN
Alheri ne ga 'yan Najeriya hana kasuwancin Bitcoin, in ji gwamnan CBN Hoto: Nairametrics
Asali: UGC

Emefiele ya kuma ba da misalin lokutan ayyukan laifi da aka bincika waɗanda ke da alaƙa da kudaden intanet. Ya ce halaccin kudi da amincin tsarin hada-hadar kudi na Najeriya su ne ginshikin aikin CBN, duk da cewa ya bayyana cewa,

“Kudaden intanet ba halattattun kuɗi ba ne” saboda ba wani Babban banki bane ya ƙirƙireshi ko ya goyi bayan amfani dashi.

Ya kara da cewa "Kudaden intanet basu da wuri a tsarin kudin mu a saboda haka a wannan lokacin kuma bai kamata a aiwatar da ma'amalar kudaden intanet ta hanyar bankin Najeriya ba."

Gwamnan Babban Bankin ya bukaci da ayi taka tsan-tsan game da lamarin kudaden intanet domin ya bada tabbacin cewa Bankin zai ci gaba da sanya ido da kuma zurfin fahimtar lamarin.

Yana mai jaddada cewa babban burin CBN shi ne yin komai cikin karfin ikonsa don ilimantar da 'yan Najeriya game da matsalolin tattalin arziki da ke kare tsarinta na kudi daga ayyukan masu barna, masu zamba ta intanet, da kuma masu damfara a duniya.

KU KARANTA: Babu wanda ya mallaki AK-47 a cikinmu, Manoma sun caccaki gwamna Lalong

A wani labarin, Hukumar Tsaro da Musaya, babbar hukuma mai kula da kasuwar babban birnin kasar, ta ce za ta hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsari na yadda za a ke hada-hada da sauran kudaden intanet (Cryptocurrencies).

Darakta-Janar na SEC, Mista Lamido Yuguda, ya fadi haka a taron hadin gwiwa na kwamitin Majalisar Dattawa kan Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Manyan Kasuwanni da harkar fasahar sadarwa da Laifukan Intanet a Abuja, ranar Talata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel