Najeriya da sauran kasashe 9 masu yawan mutane da basu da wutan lantarki

Najeriya da sauran kasashe 9 masu yawan mutane da basu da wutan lantarki

- Wasu kasashen Afrika da Asiya na fama da matsanancin rashin wutan lantarki a wasu yankuna

- Najeriya, itace ta farko a jerin kasashen da ke fama da rashin wadataccen wutan lantarki

- Rahoton mu ya tattaro kasashe 10 dake da yawan mutanen da basu da wutan lantarki a yankunansu

A shekarar 2018, Nigeria ta maye gurbin Indiya a matsayin kasar da tafi yawan jama'a ba tare da samun wutar lantarki ba.

Abu ne bayyananne a Najeriya cewa, wasu yankunan kodai basu da wutan lantarki kwata-kwata ko kuma basa samun wadatacce a yankunansu.

Kasancewar Najeriya daga cikin kasashe masu yawan cunkoso, watakila yawan mutanen ya bada gudunmawa matuka wajen rashin samun wataccen wutan lantarki, tunda Hausawa sun ce dambu idan yayi yawa bai jin mai.

Duba da ruwayar The Cable, Legit.ng Hausa ta hada muku cikakken rahoton kasashe 10 da ke da adadi mai yawa na mutanen da ke rayuwa ba tare da wutan lantarki a yankunansu ba.

KU KARANTA: Shikenan: Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

Najeriya da sauran kasashe 9 masu yawan mutane da basu da wutan lantarki
Najeriya da sauran kasashe 9 masu yawan mutane da basu da wutan lantarki Hoto: The Washington Post
Source: UGC

1. Kasar Najeriya

Kasar Najeriya a Afrika ta yamma itace a saman jerangiyar kasashen. Najeriya tana da kimanin mutane miliyan 85 da basa samun wutan lantarki.

2. Jamhuriyar Congo

A yankin Afrika ta tsakiya kuwa, jamhuriyar Congo ta kasance mai adadin mutane sama da miliyan 68 da ke fama da rashin wutan lantarki.

3. Kasar Indiya

Kasar Indiya kuwa, wacce take a kudancin Asiya ta kasance ta uku kuma mai kimanin mutane sama da miliyan 64 dake fama da duhun rashin wutan lantarki.

4. Kasar Paskistan

Mai makwabtaka da kasar ta Indiya, kasar Pakistan itace ta hudu a duniya dake fama da rashin wutan lantarki; tare da adadin mutane sama da miliyan 61 babu wuta.

5. Kasar Ethiopia

Kasar Ethiopia a gabashin Afrika ita ma na daga jerin kasashen da ke da adadi mai yawa na mutanen da basa samun wutan lantarki. Akalla mutane miliyan 60.

KU KARANTA: El-Rufai: Najeriya ta fi kowace kasa a duniya yawan talakawa

6. Kasar Tanzania

Hakazalika a gabashin Afrika, kasar Tanzania na da kimanin mutane miliyan 36 dake fama da rashin wutan lantarki.

7. Kasar Unganda

Kasar Uganda a yankin gabashin Afrika har ila yau na da adadin mutane sama da miliyan 25 dake fama da rashin wutan lantarki a yankunansu.

8. Kasar Bangladish

A dawo Asiya, kasar Bangladish na fama da rashin wutan lantarki tare da adadin mutane miliyan 24 da ke cikin duhun rashin wuta.

9. Kasar Mozambique

Mozambique hakazalika a Afrika ta gabas, itama tana fama da matsalar rashin wutan lantarki. Mutane akalla miliyan 20 ne ke fama da rashin wutan lantarki a kasar.

10. Kasar Madagascar

Karshe kasar Madagascar a gabashin Afrika na fama da wannan matsalar. Mutane sama da miliyan 19 ne ke fafutuka da rashin wutan lantarki.

A wani labarin, Yan Najeriya na ci gaba da gunaguni kan karin wuce gona da iri na kudin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta aiwatar.

NERC, wacce ta amince da karin kudin da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ta fitar, ta ce karin ya kasance tsakanin N2 zuwa N4, amma wani bangare na masu amfani da wutar da suka sake cajin mitocin su kwanan nan, sun nace cewa karin ya haura N4.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel