'Yan bindigan sun roƙi mu yafe musu', in ji wadanda aka sace a Neja

'Yan bindigan sun roƙi mu yafe musu', in ji wadanda aka sace a Neja

- Fasinjojin da masu garkuwa suka sace a karamar hukumar Rijau da ke jihar Neja daga motar NSTA sun magantu kan halin da suka shiga

- Wasu daga cikin fasinjojin sun bayyana cewa yan bindigan sun roke su da su yafe musu azabtar da su da suka yi kafin su sako su

- Fasinjojin sun bayyana cewa sun sha yunwa sosai, da rashin barci da kishin ruwa da kuma tafiya a kasa babu kakkautawa

Fasinjojin da 'yan bindiga suka sace daga cikin motar gwamnatin jihar Neja ta NSTA sun ce wadanda suka sace su sun nemi afuwarsu tare da neman su musu addu'ar shiriya kafin su sako su, rahoton The Cable.

An sace su ne a ranar 14 ga watan Fabrairu a lokacin da suke dawowa daga daurin aure a karamar hukumar Rijau da ke jihar Niger.

DUBA WANNAN: GSS Kagara: Abin da yasa soji ba za su yi fito-na-fito da ƴan bindaga ba, Tsohon direkta a DSS

'Yan bindigan sun roƙi mu yafe musu', in ji wadanda aka sace a Neja
'Yan bindigan sun roƙi mu yafe musu', in ji wadanda aka sace a Neja. @thecableng
Source: Twitter

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Niger ya sanar da sakinsu a ranar Lahadi, inda ya ce an ceto su ne sakamakon 'tattunawa da aiki tukuru'.

Da suke bada labarin irin abinda suka fuskanta a hannun yan bindigan, wasu cikin wadanda aka yi garkuwar da su sun ce yan bindigan sun tilasta musu yin tafia a kafa cikin daji a yayin da suke fama da yunwa ka kuma duka.

KU KARANTA: Nan ba da daɗewa ba Boko Haram za su iya haɗewa da ƴan bindiga, Sheikh Gumi

A rahoton NAN, Hamza Mohammed, daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya ce sun fuskanci 'ukuba' inda ya ce jarkar ruwa mai dauda daya da ake bawa shanu aka basu su goma su rika sha.

"A ranar farko, mun huta a kan dutse kuma duk wanda ya yi yunkurin yin barci zai sha bulala," in ji shi.

Mohammed ya ce ranar da za a sako su, yan bindigan sun nemi afuwarsu sannan suka roke su da su rika musu addu'ar Allah ya sa su tuba su dena abinda suke yi.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel