'Yan bindiga sun sace surukar Alhaji Ɗahiru Mangal a Katsina
- 'Yan bindiga sun kai hari gidan gidan Hajiya Rabi, surukar babban dan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal sun yi awon gaba da ita
- Mijin Hajiya Rabi, Alhaji Muntari Masanawa ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce cikin dare suka fado gidansa suka tafi da ita a babur
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, ASP Gambo Isah, da aka tuntube shi ya ce bai da masaniya kan afkuwar lamarin amma zai bincika
'Yan bindiga a safiyar ranar Talata sun tafi karamar hukumar Matazu a jihar Katsina sun sace Hajiya Rabi, surukar fitaccen dan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal.
Wani majiya daga iyalan da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa The Punch a wayar tarho a Kano cewa bata garin sun isa garin misalin karfe 1 na dare suka tafi gidan Hajiya Rabi suka yi awon gaba da ita.
DUBA WANNAN: Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA
A cewar majiyar, yan bindigan, a baya sun sace surukin danta, wani Buhari Muntari a garin Katsina.
"Yan bindigan a baya kafin su tafi Matazu sun sace mahaifin mijin yaron Hajiya Rabi a Katsina," a cewar majiyar.
Da aka tuntube shi, mijin wanda abin ya faru da ita, Alhaji Muntari Masanawa ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a wayar tarho a Kano a ranar Talata.
KU KARANTA: Manyan 'yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu a Zamfara
Muntari, wanda shine ke da sarautar 'Sarkin Yaki' a Matazu ya ce bata garin sun isa gidansa misalin karfe 1.30 na dare suka tashi matarsa suka tafi da ita a kan babur.
Ya ce sun bukaci matarsa ta biyu ta basu dukkan kudin da ta ke da shi amma ta ce bata da kudi.
Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Katsina, ASP Isah Gambo ya ce bai da masaniya kan afkuwar lamarin.
Ya ce zai bincike sannan ya kira ya bada bayani amma bai kira ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.
Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng