Mawaƙi Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa da kyautar N50,000 kowanne

Mawaƙi Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa da kyautar N50,000 kowanne

- Shahararren Mawaki Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa ta Kannywood

- Mawakin siyasan ya baiwa kowanne daga cikinsu kyautar kudi har naira 50,000

- Wannan ba shine karo na farko da mawakin ke yi wa abokan sana'ar nasa kyauta ba

Shahararren mawakin siyasa kuma shugaban mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daudu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya yi wa tsoffin jaruman masana'antar sha tara ta arziki.

A bisa ga wata wallafa da daraktan shirya fina-finai na masana'antar Kannywood, Aminu S Bono ya yi a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa Rarara ya baiwa kowannensu kyautar N50,000.

Jaruman da suka ci moriyar wannan alkhairi a maza kamar yadda ya wallafa sune: Bashir Nayaya, Moda, Isa JA, Sani Garba SK, Baba karami, Usaini Sale Koki, Baba Hasin, Shehu Hassan Kano, Ashiru na goma, Baba Sogiji, Kal’uzu Jos sai kuma Bankaura.

Mawaƙi Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa da kyautar N50,000 kowanne
Mawaƙi Rarara ya gwangwaje tsoffin ƴan wasan Hausa da kyautar N50,000 kowanne HOTO: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

A mata kuma akwai; Hajara Usman, Ladidi Fagge, Safiya Kishiya, Asma’u Sani, Hadizan Saima, Mama Tambaya, Saima Muhammed, Ladidi Tubles, Fandi Borno, Baba Duduwa, Hajiya Sadiya, Lubabatu Madaki da Hajiya Olah.

Wannan ba shine karo na farko da yake haka ba, domin a baya ma Rarara ya gwangwaje wasu daga cikin jaruman masana’antar da kyautar sabbin motoci.

Daga cikin wadanda Rarara yayi wa kyautar akwai Jamila Nagudu da Tijjani Asase, ya kuma basu motoci kirar Toyota Matrix ne.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin real_rarara_multimedia ta Instagram, an gano jaruma Jamila Nagudu cike da farin ciki da murna a lokacin da Rarara ke mika mata mukullin motar da ya mallaka mata.

Hakazalika an gano Tijjani Asase shima yana karbar tasa mukullin motar cike da farin ciki.

A wani labarin kuma, tsohuwar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa'a tayi martani mai zafi a kan masu zuwa yawon shakatawa kasar Dubai sannan suke wallafa hotunansu.

Rashida ta bayyana hakan a matsayin kauyanci da rashin sanin ciwon kai inda tace ita kasuwar Rimi ya ma fiye mata zuwa Dubai din.

Manyan jaruman masana'antar Kannywood irin su Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Fati Washa da sauransu na can a kasar Dubai suna shakatawa.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel