Shugaba Buhari ya canza dogarinsa, ya zabi Dodo

Shugaba Buhari ya canza dogarinsa, ya zabi Dodo

- Buhari ya canza mutumin da ke bin shi kusan duk inda yake a koda yaushe

- Wannan ne karo na farko da Buhari ya canza ADC din shi tun da ya hau mulki

Shugaba Muhammadu Buhari ya canza dogarinsa wanda akafi sani da ADC, kuma ya zabi sabon ADC, Channels TV ta jiyo daga fadar shugaban kasa.

Laftanan Kanal Y. M Dodo zai maye Kanal Muhammed Abubakar, wanda ya ke tsare Buhari tun 2015.

A cewar majiyoyin, Kanal Abubakar zai ajiye aikinsa ne saboda halartan wani kas domin ya samu karin girma zuwa matsayin Birgediya Janar.

Laftanan Kanal Dodo ya kasance hadimi ga kwamandan makarantar Sojoji NDA dake Kaduna.

Yanzu haka shugaba Buhari na garinsa, Daura, domin musharaka a shirin sabunta rijistan kasancewa mamba jam'iyyar.

KU DUBA: COVID-19: Jihohi 7 a arewacin Najeriya za su mori tallafin $900,000

Shugaba Buhari ya canza dogarinsa, ya zabi Dodo
Shugaba Buhari ya canza dogarinsa, ya zabi Dodo
Asali: Facebook

KU DUBA: Shugaba Buhari ya sake shillawa Daura, jihar Katsina

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 30 ga watan Junairu, 2021, ya jaddada rijistarsa a matsayin mamban jam'iyyar All Progressives Congress APC a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin nan inda yace: "Yau a Daura, na yi musharaka a shirin rijista da jaddada rijistan jam'iyyarmu mai girma APC."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng