Rarara ya gwangwaje jaruman Kannywood da kyautar sabbin motocin alfarma
- Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya rabawa wasu daga cikin jaruman Kannywood sabbin motoci kyauta
- A wannan karon, rabon ya hau kan Jamila Nagudu da Tijjani Asase ne inda ya basu mota kirar Toyota Matrix
- Dama dai Rarara ya saba yiwa abokan sana'ar tasa sha tara ta arziki lokaci zuwa lokaci
Fitaccen mawakin nan na siyasa kuma Shugaban mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje wasu daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood da kyautar sabbin motoci.
Daga cikin wadanda Rarara yayi wa kyautar akwai Jamila Nagudu da Tijjani Asase, ya kuma basu motoci kirar Toyota Matrix ne.
Ba wannan ne karo na farko da fitacen mawakin ke yi wa jaruman masana’antar sha tara ta arziki ba.
KU KARANTA KUMA: Hanan Buhari ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kalaman soyayya
Lokuta da dama, su kan fito su nuna jinjina da yabawa a kan wani abun azo a gani da yayi musu a shafukansu na zumunta.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin real_rarara_multimedia ta Instagram, an gano jaruma Jamila Nagudu cike da farin ciki da murna a lokacin da Rarara ke mika mata mukullin motar da ya mallaka mata.
Hakazalika an gano Tijjani Asase shima yana karbar tasa mukullin motar cike da farin ciki.
Abokanan aikin wadannan jarumai sun yi wa mawakin ambaliyar addu’o’in Allah ya saka da Alkhairi.
A wani labarin kuma, tsohuwar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa'a tayi martani mai zafi a kan masu zuwa yawon shakatawa kasar Dubai sannan suke wallafa hotunansu.
KU KARANTA KUMA: Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa
Rashida ta bayyana hakan a matsayin kauyanci da rashin sanin ciwon kai inda tace ita kasuwar Rimi ya ma fiye mata zuwa Dubai din.
Manyan jaruman masana'antar Kannywood irin su Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Fati Washa da sauransu na can a kasar Dubai suna shakatawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng