Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sake sauya sheka zuwa APC

Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sake sauya sheka zuwa APC

- Hon Peter Makinde dan majalisar da ke wakiltar Ondo ta gabas da yamma a majalisar wakilai ya sauya sheka daga ADC zuwa APC

- Makinde ya ce ya koma jam'iyya mai mulki ne saboda rikicin da ya dabaibaye tsohuwar jam'iyyarsa

- Sai dai an dan samu takkadama kan sauyin shekar nasa saboda rashin hallaran shugabancin kwamitin marasa rinjaye a majalisar

Dan majalisar da ke wakiltar Ondo ta gabas da yamma a majalisar wakilai, Hon Peter Makinde a ranar Talata, 23 ga watan Fabrairu, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga African Democratic Congress (ADC).

Sai dai mambobin kwamitin marasa rinjaye a majalisar sun yi adawa da sauyin shekar Makinde a bayan idon dukkanin shugabanninsu wadanda basu hallara ba a lokacin da aka sanar da sauyin shekar nasa.

A wata wasika da Kakakin majalisar, Hon. Femi Gbajabiamila ya karanto a zauren majalisar, Hon. Makinde ya ce ya yanke shawarar barin ADC ne sakamakon rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a dukkan matakai.

Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sake sauya sheka zuwa APC
Yanzu Yanzu: Wani dan majalisar wakilai ya sake sauya sheka zuwa APC Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Muna matuƙar buƙatar mazajen aure, ƴan matan Gombe sun koka

Kafin karanto wasikar, Kakakin majalisar ya nemi wasu mambobin kungiyar marasa rinjaye da su cike kujerar Shugabancin Marasa Rinjayar tunda babu ko daya daga cikinsu da ya kasance a zauren.

Sai dai kuma, Hon. Ossai Nicholas Ossai wanda ya yi magana a madadin kwamitin ya ce matakin ya sabawa sashi na 68 na kundin tsarin mulkin 1999 kamar yadda aka yi kwaskwarima, ya kara da cewa kakakin Majalisar ya yi abin da ya kamata ta hanyar ayyana kujerar a matsayin babu kowa.

Ossai (PDP, Delta) ya ce daga cikin abin da dokar ta tanada shi ne, dole ne mutumin da ya sauya sheka daga jam’iyyarsa da ta dauki nauyin zabensa ya gabatar wa majalisar shaidar dalilin da ya sa ya sauya shekar.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun sace babban basarake a Ribas, har yanzu ba a san inda yake ba

Da yake mayar da martani, kakakin majalisar Gbajabiamila ya ce shaidar sauya sheka da take kunshe a cikin kundin tsarin mulki na iya zama ta fatar baki, yana mai cewa “Yanzu haka na karanta wasikar da dan majalisar ya rubuta a kan dalilin da ya sa ya sauya sheka. Tunda na kasance a wannan majalisar, wannan shi ne tsari koyaushe.”

Ya tambayi Ossai ko yana sane da waye Shugaban Jam’iyyar ADC na kasa, ya kara da cewa “tunda ba ka san sunan Shugaban Jam’iyyar da ya sauya sheka ba, hakan ya sa ka zama mai shiga tsakani a Doka don haka, ba ka da hurumin jan hankalin. Don haka an kore ka daga odar."

'Yan mintoci kaɗan bayan yanke hukuncin, sai wasu mambobin kwamitin Shugabancin Marasa Ruwa a karkashin jagorancin Hon. Ndudi Elumelu suka shigo cikin zauren.

A gefe guda, gabanin babban zaben 2023, jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta fara kamfen don janyo hankalin masu ruwa da tsaki su kafa kwakwarar jam'iyya da za ta iya fafatawa da manyan jam'iyyu biyu na kasar, rahoton Daily Trust.

Jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a halin yanzu sune manyan jam'iyyun siyasa a kasar.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin taron musayar ra'ayi na jam'iyyar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, ya ce jam'iyyarsu za ta tafi da kowa ba irin siyasar uban gida da ake yi ba a sauran jam'iyyu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel