Jam'iyyar PRP ta fi APC da PDP, in ji Farfesa Attahiru Jega

Jam'iyyar PRP ta fi APC da PDP, in ji Farfesa Attahiru Jega

- Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Farfesa Attahiru Jega yace jam'iyyar PRP za ta fi zama alheri ga yan Nigeria a maimakon APC da PDP

- Attahiru Jega ya bayyana hakan ne yayin taron musayar ra'ayi na masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PRP a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi

- Tsohon shugaban hukumar INEC ya ce ya yi gargadi kan illar da siyasar mai gida ke yi wa Nigeria inda ya ce babu wannan a PRP

Gabanin babban zaben 2023, jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta fara kamfen don janyo hankalin masu ruwa da tsaki su kafa kwakwarar jam'iyya da za ta iya fafatawa da manyan jam'iyyu biyu na kasar, rahoton Daily Trust.

Jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a halin yanzu sune manyan jam'iyyun siyasa a kasar.

Jam'iyyar PRP ta fi APC da PDP, in ji Farfesa Attahiru Jega
Jam'iyyar PRP ta fi APC da PDP, in ji Farfesa Attahiru Jega. @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: GSS Kagara: Abin da yasa soji ba za su yi fito-na-fito da ƴan bindaga ba, Tsohon direkta a DSS

Shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin taron musayar ra'ayi na jam'iyyar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, ya ce jam'iyyarsu za ta tafi da kowa ba irin siyasar uban gida da ake yi ba a sauran jam'iyyu.

Jega, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ya ce siyasar uban gida ta mamaye siyasar Nigeria kuma ta yi wa kasar illa.

KU KARANTA: Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a Neja sun magantu

Ya ce bisa la'akari da yadda abubuwa da ke tafiya a jam'iyyarsa da kuma yadda al'umma ke rungumar ta a sassan kasar, yana kyautata zaton yan PRP za ta fi alheri ga yan Nigeria.

A kan batun takarar 2023, Jega ya ce ba yanzu ne lokacin da za a yi wannan batun ba, inda ya ce idan an saka batun takara a gaba, za a manta da batun saita jam'iyyar kan alkibla mai kyau.

"Muna sake yi wa jam'iyyar tsari mai kyau ne domin hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki, hakan yasa muka shirya wannan taron musayar ra'ayin ga masu ruwa da tsaki a jihar Kebbi.

"Muna aiki domin ganin mun gina jam'iyyar da za ta zama zabi ga 'yan Nigeria gabanin 2023 a maimakon manyan jam'iyyu biyu masu rinjaye a kasar," in ji shi.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel