'Yan bindiga sun sace babban basarake a Ribas, har yanzu ba a san inda yake ba

'Yan bindiga sun sace babban basarake a Ribas, har yanzu ba a san inda yake ba

- Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani basarake a jihar Ribas

- An yi garkuwa da Aaron Ikuru lokacin da wadanda suka sace shi suka kai mamaya fadarsa a ranar Lahadi

- ‘Yan sanda sun ce ana ci gaba da kokarin kubutar da basaraken

Al’ummar Ikuru da ke karamar hukumar Andoni a jihar Ribas sun shiga cikin halin fargaba sakamakon sace sarkin garin Aaron Ikuru da yan bindiga suka yi.

Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun ce wasu masu garkuwa da mutane da ba a san ko su wanene ba sun kai mamaya fadar sarkin inda suka dauke shi zuwa wani wurin da ba a sani ba.

KU KARANTA KUMA: Ba dan ta'adda bane: FKK ya ambaci gwamnan arewa da ya taimaki Jonathan ya zama shugaban kasa bayan 'Yar'adua

Tsoro a Ribas yayin da 'yan bindiga suka sace babban basarake, har yanzu ba a san inda yake ba
Tsoro a Ribas yayin da 'yan bindiga suka sace babban basarake, har yanzu ba a san inda yake ba @PremiumTimesng
Source: UGC

Ba a tuntubi dangin sarkin ba kan yiwuwar biyan kudin fansa, jaridar Sun ta ruwaito.

Da yake maida martani kan lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya ce an dukufa don gano sirrin da ke tattare da satar.

Omoni ya ci gaba da cewa ana nan ana aiki tukuru don tabbatar da ganin an saki basaraken daga kogon wadanda suka sace shi.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayyana ainahin dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu

A gefe guda, fasinjojin da 'yan bindiga suka sace daga cikin motar gwamnatin jihar Neja ta NSTA sun ce wadanda suka sace su sun nemi afuwarsu tare da neman su musu addu'ar shiriya kafin su sako su, rahoton The Cable.

An sace su ne a ranar 14 ga watan Fabrairu a lokacin da suke dawowa daga daurin aure a karamar hukumar Rijau da ke jihar Niger.

Da suke bada labarin irin abinda suka fuskanta a hannun yan bindigan, wasu cikin wadanda aka yi garkuwar da su sun ce yan bindigan sun tilasta musu yin tafia a kafa cikin daji a yayin da suke fama da yunwa ka kuma duka.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel