FG ta bayyana ainahin dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu

FG ta bayyana ainahin dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu

- Gwamnatin tarayya ta maida martani game da sakin Leah Sharibu da kungiyar Boko Haram ta ki yi

- Lai Mohammed ya bayyana abin da gwamnati ke yi don ganin ta ceto ‘yar makarantar Dapchin daga hannun‘ yan Boko Haram

- Ministan yada labaran da al'adu ya soki yadda wasu 'yan Najeriya ke kallon al'amuran tsaro

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa da gangan ‘yan ta’addan Boko Haram suka ki sakin Leah Sharibu domin raba kan‘ yan Najeriya ta bangaren addini.

Leah Sharibu, yar kirista, ta kasance daga cikin dalibai mata 110 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, Dapchi a jihar Yobe da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar 2018.

Musamman lamarinta ya ja hankalin al’umman kasar da na duniya baki daya, saboda yadda aka saki wasu amma ita aka tsare ta saboda ta ki yin watsi da addininta na Kirista.

FG ta bayyana dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu
FG ta bayyana dalilin da ya sa kungiyar Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu Hoto: @FMICNigeria, @GaryLCain1
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Yanzu makiyaya da manoma duk sun mallaki AK-47, Lalong

Sai dai, Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu na Najeriya ya fada wa gidan talabijin na Channels TV cewa ‘yan ta’addan sun san cewa rike Sharibu a hannunsu na iya haifar da rikicin addini a kasar.

Ministan ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya na ta kokari ta kofar baya don ganin an sako‘yar makarantar Dapchin.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da kar su yi yarda su fada tarkon ‘yan ta’adda ta hanyar kallon al’amuran tsaro ta fuskar addini ko kabilanci.

Mohammed ya ce:

“Don Allah ya zama dole mu kiyaye kuma mu kula sosai a kan yadda muke kallon al'amura. Wannan shi ne ainihin abin da 'yan ta'addar ke so su yi, su hada Musulmi da Kirista.”

KU KARANTA KUMA: Wanda za a cafke idan aka hallaka ni shi ne Gwamnan Bauchi – Gwamna Ortom

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Fasto Enoch Adejare Adeboye, wanda ya kafa kuma shugaban cocin Redeem Christians Church of God (RCCG), ya yi kira da a saki Leah Sharibu.

Sharibu, wacce ta kasance kirista mai shekaru 14 a lokacin da aka kama ta, ita kadai ce yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan ta’addan bayan mamayar da Boko Haram ta kai masu a garin Dapchi da ke jihar Yobe a 2018.

An ruwaito cewa ta ki yarda ta bar addininta a lokacin da wadanda suka sace ta suka yi kokarin musuluntarta ta karkin tuwo.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel