Farashin man fetur zai iya cillawa zuwa N200, sakamakon tashin farashin danyen mai zuwa $64

Farashin man fetur zai iya cillawa zuwa N200, sakamakon tashin farashin danyen mai zuwa $64

- Farashin man fetur ya haura N186 a makon nan, sakamakon wasu sauye-sauye a kasuwar

- A makwannin baya dai man ya cilla zuwa wani farashi da muka ambata a wani rahoton

- Farashin nada alaqa da canjin farashin danyen mai a kasuwar duniya da kuma faduwar Naira a duniya

Dangane da yadda farashin mai ya hauhawa, farashin sauka da farashin Man Motoci na Fetur (PMS) ya haura zuwa N186.33 a kowace lita, The Punch ta ruwaito.

A baya mun bayar da rahoto ne a ranar 9 ga Fabrairu cewa farashin na PMS ya tashi zuwa kusan N180 kowace lita a ranar 5 ga Fabrairu daga N158.53 kowace lita a ranar 7 ga Janairu.

Farashin danyen mai ya kawo kaso mafi tsoka na kudin karshe na man fetur, da kuma rage farashin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi a bara ya nuna cewa farashin famfo na kayan zai nuna canji a kasuwar mai ta duniya.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta bada umarnin kame shugaban NDDC saboda cinye tallafin Korona N6.25bn

Farashin man fetur ya cilla zuwa N186, mai a kasuwar mai ta duniya ya kai dala 64
Farashin man fetur ya cilla zuwa N186, mai a kasuwar mai ta duniya ya kai dala 64 Hoto: DW
Asali: UGC

Idan aka tafi da samfurin farashin mai na Hukumar Kula da Farashin Kayayyakin Man Fetur, farashin saukar da mai ya tashi zuwa N186.33 a kowace lita a ranar 16 ga Fabrairu, inda ake sa ran farashin na bakin famfo zai zama N209.33 a kowace lita.

Farashin danyen mai na kasa da kasa, danyen mai na Brent, an rufe shi a $63.96 a kowace ganga a ranar 16 ga Fabrairu, daga $59.34 kan kowace ganga a ranar 5 ga Fabrairu.

Karin farashin danyen mai ya sanya farashin man fetur da aka ambata a kan Platts zuwa $560.75 a kowace metric tonne (N163.08 a kowace lita, ta amfani da N390/$ 1) a ranar 16 ga Fabrairu daga $543.25 a kowace metric tonne (N157.99 kowace lita) a ranar 5 ga Fabrairu.

Baya ga canjin da aka samu a farashin danyen mai a duniya, canjin naira zuwa dala ma na shafar farashin man fetur da ake shigowa da shi.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na gwangwaje tsofaffi da kyautar awaki, in ji Dan Majalisa

A wani labarin, Yan Najeriya na ci gaba da gunaguni kan karin wuce gona da iri na kudin wutar lantarki da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta aiwatar.

NERC, wacce ta amince da karin kudin da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ta fitar, ta ce karin ya kasance tsakanin N2 zuwa N4, amma wani bangare na masu amfani da wutar da suka sake cajin mitocin su kwanan nan, sun nace cewa karin ya haura N4.

Aminiya ta tattauna da ’yan Najeriya don gano yadda hawan ya shafi amfani da wutar lantarki da suke yi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel