Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya

Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya

- An samu bayanai akan jirgin da injinsa ya lalace ya fado daga sama yayi sanadiyyar mutuwar mutane 7

- Dama duk sojojin sama na Najeriya NAF201, ne cikin jirgin suna neman inda 'yan Kagara da aka sace suke

- Suna tsaka da neman ne injin jirgin ya lalace da misalin 10:39am ya fado tantagaryar titin garin Abuja

Ashe sojojin sama na NAF201 da suka yi hatsari a jirgin sama, har mutane 7 da matukan jirgi da suka mutu a Abuja, suna neman wadanda aka sace a Kagara ne, kamar yadda bayanai suka bayyana a ranar Lahadi da yamma.

Kamar yadda aka samu labari, bayan kara wa jirgin mai a Abuja, jirgin ya bazama neman 'yan makarantan Kagara da aka sace ne a jihar Neja, Vanguard ta wallafa.

"Jirgin ya nufi Abuja don shan mai, injin jirgin ya samu matsala yayin da ya keta hazo ya kasa sakkowa duk da kokarin da yayi don sauka lafiya."

KU KARANTA: Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu

Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya
Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Labarai sun kammala akan yadda hafsin sojin sama suka rasu a filin jirgin. Muna fatan Ubangiji yayi musu rahama, sun mutu yayin yi wa kasa bauta.

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya sanar da yadda lamarin ya faru inda yace injin jirgin ya lalace ne da misalin 10:39am sannan ya fadi kasa ne a tantagaryar titin filin jirgin sama Abuja Runway 22.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara

A wani labari na daban, shaguna masu tarin yawa da ke kasuwar siyar da safayan kayan motoci da ke titin Jos a yankin Oriapata da ke jihar Kaduna sun babbake sakamakon gobarar da ta tashi.

Duk da har yanzu ba a gano musababin wutar ba da ta tashi a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 'yan kasuwa da mazauna yankin sun tabbatarwa da Channels TV cewa gobarar ta fara ne bayan da wani shago daya ya fara babbaka.

Shugabannin kungiyar 'yan kasuwan masu siyar da bangarorin motocin sun ce gobarar ta yi mummunar barna tunda ta shafi kayan kudi masu tarin yawa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: