NALDA zata tallafawa masu kiwon kifi 2,000 a jihar Borno da wasu 1,040
- Gwamnantin tarayya karkashin shirin NALDA zata tallafawa manoma kifi 2,000 a jihar Borno
- Za kuma shirin ya tallafawa wasu 1,040 daga cikin masana kimiyyar kasar noma a cikin jihar
- An bayyana cewa, za a fara gudanar da shirin wa wata mai zuwa a cikin jihar ta Borna a arewacin Najeriya
Babban sakatare na hukumar bunkasa filayen noman kasa (NALDA), Prince Paul Ikonne, ya ce hukumar na su zata dauki kimanin manoman kifi 2,000 kuma za ta fara horar da masana kimiyyar kasa 1,040 a jihar ta Borno, Daily Trust ta ruwaito.
Ikonne ya fadawa manema labarai a Abuja bayan ganawa da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, cewa tattaunawar tsakanin NALDA da Gwamnatin jihar Borno “a kan shirinmu na kiwon kifi, wanda muke sa ran manoma sama da 2,000.”
KU KARANTA: 2023: Jerin manyan arewa dake goyon bayan mayar da mulkin Najeriya Kudu
“Jihar Borno ta gabatar da cikakken jerin sunayensu kuma ta samar da wurare. Yayinda muke magana, yan kwangila sun riga sun kasance a wurin kuma a wurare 10 don aikin.
"Don haka gwamnan jihar Borno ya yi cikakken bayani game da tunanin Shugaban kasa na cimma wadatar abinci, ba tare da la’akari da kalubalen da jihar ke fuskanta ba. Gwamnan yana saukakawa NALDA wajen aiki sannan manoma su kasance a gida yayin da suke noma,” inji shi.
NALDA (hukumar da ke karkashin shugabancin kai tsaye) a watan da ya gabata ta sanar da amincewar shugaban don shigar da masana kimiyyar kasar gona 30,000 da masu aikin fadadawa a duk fadin kasar.
Za a fara gudanar da horon ne a jihar Borno a farkon watan gobe.
Ya ce hukumar tana mai da hankali kan kusan komai a dukkanin sassan jihar saboda suna da kyawawan abubuwan more rayuwa da kayan aiki da kuma injinan sarrafawa.
KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro shirin kula da masu Korona daga gida
A wani labarin, Mista Ezra Amos, mai shekara 70 kuma tsohon ma'aikacin gwamnati daga yankin Dadin Kowa na Jihar Gombe ya ce ya samu sama da Naira miliyan 3 daga noman kifi a shekarar 2020.
Amos, wanda ya yi magana a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Dadin Kowa, karamar Hukumar Yamaltu-Deba, ranar Laraba, ya ce noman kifi yana biyan bukatunsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng