‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina

- Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mata 13 a yankin karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina

- An tattaro cewa matan na a hanyarsu ta zuwa karbar tallafi da suka samu ne lokacin da maharan suka bude masu wuta

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin, sai dai ta ce uku daga cikinsu sun tsere daga bisani

Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zaton ‘yan bindiga ne sun kai mamaya yankin karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina inda suka yi garkuwa da wasu mata zuwa cikin jeji.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar afkuwar al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Ba da jimawa ba za a saki daliban Kagara da aka sace, in ji shugaban ‘yan fashin Zamfara

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina
‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina @PremiumTimesng
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Isah Gambo ya ce maharan sun bude wa motar da matan ke ciki kirar Golf wuta a kan hanyarsu zuwa banki a Funtua domin karbar tallafin da suka samu.

Ya kuma ce yan bindigan sun yi cikin jeji da mata 13 wadanda suka fito daga garin Maigora amma daga bisani uku daga cikinsu sun tsere.

A cewar rundunar yan sandan an kai harin ne a safiyar ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba"

A gefe guda, wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe makiyayi da direban babban mota a Kajuru, Karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, a cewar Mr Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaro da harkokin gida, Vanguard ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, Aruwan ya ce yan bindigan suna tserewa su koma cikin daji ne a kusa da kauyen Doka a karamar hukumar Kajuru, suka kashe makiyayin suka dauke babur dinsa da wasu kayayaki.

Ya yi bayanin cewa jami'an tsaro na bin sahun yan bindigan, yayin da an dauko gawar makiyayin an mika wa iyalansa don su yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel