Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba"

Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba"

- Fasto Adeboye ya yi kira ga cocina da kada su hakura da bukatar su na sakin Leah Sharibu

- Faston wanda ya kasance shugaban RCCG ya yi rokon ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin ganin ta ceto yaran makarantar Kagara

- ‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi garkuwa da Sharibu a shekarar 2018 a garin Dapchi, kuma ba a sake ta ba bayan ta ki yarda ta bar addininta

Enoch Adejare Adeboye, wanda ya kafa kuma shugaban cocin Redeem Christians Church of God (RCCG), ya yi kira da a saki Leah Sharibu.

Sharibu, wacce ta kasance kirista mai shekaru 14 a lokacin da aka kama ta, ita kadai ce yar makarantar Dapchi da ta rage a hannun yan ta’addan bayan mamayar da Boko Haram ta kai masu a garin Dapchi da ke jihar Yobe a 2018.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba"
Fasto Adeboye yayi kira da a saki Leah Sharibu, ya ce "ba za mu saduda ba" Hoto: @PastorEAAdeboye
Asali: Twitter

An ruwaito cewa ta ki yarda ta bar addininta a lokacin da wadanda suka sace ta suka yi kokarin musuluntarta ta farkin tuwo.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Juma’a, 19 ga watan Fabrairu, shahararren malamin na Kirista ya ce cocina ba za su yi kasa a gwiwa ba a kokarinsu na neman a saki Sharibu.

Kiran da Adeboye ya yi na a saki Sharibu ya zo ne sa’o’i 48 bayan sace daliban a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, jihar Neja. Ana ci gaba da kokarin ceto su.

KU KARANTA KUMA: Manyan nade-nade guda 6 da Shugaba Buhari yayi a cikin satin da ya gabata

"A nan ina sake kira tare da umurtar duk fastocin da ke cikin Redeemed Christian Church of God, a duk faɗin duniya, da kada su tsaya illa su ƙara tsananta addu'o'insu don sakin Leah Sharibu.

Ina kuma kira ga dukkan iyaye, a duk fadin duniya, da su yi amfani da duk wani tasiri da suke da shi, don tabbatar da cewa an saki Leah Sharibu, da sauran yara da ke tsare. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba a addu'o'inmu."

A wani labarin, wani babban dan bindiga a jihar Zamfara ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a saki malamai da daliban Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara da aka sace a jihar Neja.

Dan fashin, Dogo Gide, wanda ke jar ragamar kula da dajin kudancin Zamfara ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da jami'an gwamnatin jihar Neja, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, duk da cewa wadanda aka sacen ba su a sansaninsa, zai tattauna da sauran 'yan ta'addan don hanzarta sakinsu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel