Manyan nade-nade guda 6 da Shugaba Buhari yayi a cikin satin da ya gabata
- Ana cikin lokaci na nade-naden mukaman siyasa a Najeriya
- Kamar yadda muka sani wa'adin mulkin mutane da dama da aka ba mukamai a cikin gwamnatin tarayya ya kare ko yana shirin karewa
- Ya zama dole shugaban kasa ya maye gurbin wadannan mukamai, kuma a satin da ya gabata, an samu sabbin shugabanin da aka nada a manyan wurare
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi muhimman nade-nade na mukaman gwamnati guda shida a cikin makon da ya gabata.
Nade-naden sun kasance a fadin hukuma da kuma bangarori daban-daban da suka hada da hukumar sojoji, fannin cire kudi da bangaren kudi.
Ana sa ran samun karin nade-nade a cikin makonni masu zuwa yayin da wa'adin sauran wadanda aka nada ke zuwa karshe.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza
Legit.ng ta jero nade-nade shida da shugaban kasa yayi a makon da ya gabata:
1. Manjo-Janar Samuel Adebayo
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI) kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa(DIA). Ya gaji Air Vice Marshal Muhammed Usman, wanda ya yi ritaya.
2. Mista Aghughu Adolphus A.
Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Aghughu Adolphus a matsayin babban mai binciken kudaden na gwamnatin tarayya, AGF, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban ya mika takardar nadin ga shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan kamar yadda sashe na 86 (1) na kundin tsarin mulki ya tanada.
3. Dr Ogbonnaya Orji
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Orji Ogbonnaya Orji a matsayin sabon shugaban hukumar Nigeria Extractive Industries Transparency Initiative (NEITI).
Shugaban kasa ya nada Dr. Orji Ogbonnaya Orji ne bayan Waziri Adio ya kammala wa’adinsa na tsawon shekaru biyar a jiya ranar Alhamis, 18 ga watan Fubrairu, 2021.
KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana
4. Abudulrasheed Bawa
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin zababben shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.
5. Ahmed Abubakar Audi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ahmed Abubakar Audi a matsayin sabon babban kwamandan hukumar tsaro da NSCDC da aka fi sani da Civil Defence.
Nadin ya zo ne bayan murabus din da tsohon shugaban hukumar ta NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu ya yi.
6. Haliru Nababa
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Haliru Nababa mni a matsayin sabon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali.
A wani labarin, babban bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu ya ba mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tabbacin cewa Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, zai dawo jam’iyyar mai mulki nan ba da dadewa ba.
Kalu ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan Wike ya jagorance shi a yayin duba wani aiki a Port Harcourt, babban birnin jihar a ranar Alhamis, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wasu daga cikin ayyukan da aka duba sun hada da gadar sama na Rumuokoro, gadar sama na biyu na Artillery, makarantar kwallon kafa na Real Madrid da kuma asibitin Mother and Child Hospital a Rumuomasi.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng