Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo

Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo

- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce ko wanne dan Nigeria na da ikon zama duk inda ya ke so

- Gwamnan ya fadi hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television game da batun korar makiyaya daga jihar Ondo

- Gwamnan ya ce sashi na 42 na kundin tsarin mulkin kasa ya bawa duk dan Nigeria zama a inda ya ke so ba tare da neman izinin gwamna ko shugaban kasa ba

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce yan Nigeria ba su bukatar izinin wani gwamna kafin su zauna a ko wanne yankin kasar.

A cewar Mohammed, yan kasa ba su bukatar izinin takwararsa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu kafin su zauna a dazukan da ke jihar ta Kudu ta Maso Yamma.

Yanzu-yanzu: Ɗan majalisar Kano na jamhuriya ta biyu, Dr Junaid Mohammed ya rasu

Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo
Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Gwamnan na Bauchi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television a shirin 'Sunrise Daily' da Legit.ng Hausa ta bibiya.

KU KARANTA: Sheikh Gumi: Za a sako waɗanda aka sace a GSC Kagara nan ba da daɗewa ba

Ya ce, "Kasa a hannun gwamnatocin jihohi da tarayya su ke amma yan Nigeria ba su bukatar izinin gwamnatin jiha ko tarayya kafin su zauna a ko ina. Ba ka bukatar izinin gwamnan Bauchi ko Ondo kafin ka zauna a dajin Ondo idan kana son zama a dajin domin karkashin sashi na 42 na kudin tsarin mulki, kana da ikon zama a ko ina."

Tunda farko, gwamnan Ondo, a kokarinsa na kawo zaman lafiya a jiharsa ya bukaci makiyaya da ke dazukan su yi rajista ko kuma su fice daga jihar sakamakon zargin da ya ke yi na cewa makiyaya ne ke kai hare-hare a jiharsa.

Akeredolu ya kuma soki furucin da gwamnan Bauchin ya yi na cewa makiyaya suna da damar daukan makami domin kare kansu da dabbobinsu daga hare-hare.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164