Sheikh Gumi: Za a sako waɗanda aka sace a GSC Kagara nan ba da daɗewa ba
- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce za a sako dalibai da ma'aikatan GSC Kagara da aka sace
- Hakan na zuwa ne bayan tattakin da malamin da tawagarsa suka tafi dazuka suka gana da shugabannin yan bindiga ciki har da Gide Dogo
- A baya bayan nan, Sheikh Gumi ya shiga sahun wadanda suke kira ga gwamnati ta yi wa yan bindiga afuwa ta basu tallafi saboda rashin adalcin da aka musu
Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Gumi ya bada tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za a sako wadanda yan bindiga suka sace a makarantar kwallejin kimiyya ta Niger.
Gumi ya yi wannan jawabin ne bayan ganawar da ya yi da yan bindiga a dazukan Tegina da Birnin Gwari a jihar Kaduna, The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
Majiya, daga cikin tawagar da suka hallarci taron, ta ce Sheikh Gumi ya gana da shugaban yan bindigan, Dogo Gide, da wasu shugabannin yan bindiga a dajin Dutsen Magaji.
Majiyar ta ce gwamnati ta aike da tawaga mai karfi domin ganawa da yan bindigan da nufin yin sulhu da su.
Har wa yau, majiyar ta ce Sheikh Ahmed Gumi da tawagarsa suna kan hanyarsu na komawa gida daga Minna, babban birnin jihar Neja.
KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa
Gumi ya na shawartar gwamnati ta yi wa yan bindiga afuwa kamar yadda ta yi wa tsagerun yankin Neja Delta, inda ya ce rashin adalcin da aka yi wa makiyaya ne ya janyo suka dauki makamai.
Sai dai wannan matsayar ta Gumi ya janyo masa suka daga shugabannin kungiyoyin yankunan Yarbawa, Ibo da jihohin Tsakiya.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng