Rashin tsaro ya zama kasuwanci ga wasu 'yan Nigeria, in ji Solomon Dalung
- Tsohon ministan Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dalung ya yi fashin baki kan tabarbarewar tsaro a Nigeria musamman satar dalibai
- Da ya ke magana game da satar daliban makarantar Kagara da ya faru a baya-bayan nan, ya ce akwai sakaci daga hukumomin tsaro sannan akwai siyasa
- Tsohon ministan ya ce akwai wasu yan siyasan da kokarinsu shine muzanta Shugaba Muhammadu Buhari duba da cewa shine jama'a suka wa kalon zai iya dai-daita kasar
Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.
A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.
DUBA WANNAN: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa
A cewar Dalong akwai wadanda suka maida rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.
"Idan an dawo siyasa, ita siyasa itace ta gurbacce harkar tsaro a ko ina a arewa domin siyasa ta samu shiga a cikinta fiye da yadda ake tsamanni kuma ita harkar tsaron nan ta zama kasuwanci, akwai yan kasuwan wadanda suke cin moriya da rigingimu da suke faruwa a arewa, su idan anyi zaman lafiya, za su yi kwanan yunwa amma idan ana nan ana rigima ana kashe-kashe, ana sace- sace, to kakarsu ta yanke saka.
"Siyasan da ke cikin lamarin shine akwai wadanda ke ganin Shugaba Muhammadu Buhari tunda ya ce ya iya, toh bari a bar shi ya yi mu gani, saboda haka yan siyasa a maimakon a hada kai a hada hannu a gani cewa babban barazana ce za ta shafe mu a matsayin al'umma toh ana kokarin kowanne rana, a gani cewa an dawo da mutunci da martabar na shugaban kasa, kasa domin irin yadda jama'a suka nuna cewa shine kadai ya iya," a cewar Dalung.
KU KARANTA: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
Tsohon ministan ya shawarci al'umma su yi watsi da irin wannan mumman siyasar da ba za ta haifar da alheri ba sai dai kai kasar ga mummunan alkibla.
Ya kuma mika sakon jajensa ga wadanda aka sace musu yara tare da fatan Allah ya sa a ceto su lafiya tare da kira ga gwamnatin tarayya, na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki su hadda hannu wurin tsaftace siyasa da hadin kan kasa.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng