Yanzu-yanzu: Ɗan majalisar Kano na jamhuriya ta biyu, Dr Junaid Mohammed ya rasu
- Allah ya yi wa fitaccen dan siyasa kuma tsohon dan majalisar Kano a jamhuriya ta biyu, Dr Junaid Mohammed rasuwa
- Dr Junaid Mohammed ya rasu a daren ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Daya daga cikin yayansa mai suna Suleiman ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa da ya ce ya rasu yana da shekaru 73 a duniya
Dan majalisa na Jamhuriya ta biyu mai wakiltar Kano, Dakta Junaid Mohammed ya riga mu gidan gaskiya, The Vanguard ta ruwaito.
Dan marigayin, Suleiman ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce ya rasu a daren ranar Alhamis yana da shekaru 73 a duniya bayan fama da rashin lafiya na kwanaki uku.
Iyalansa za su sanar da ranar da za a yi jana'izarsa.
DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
Ministan saka hannun jari da cinikayya, Otunba Adeniyi Adebayo da wasu masu zuwa ta'aziyya sun fara tururuwa zuwa gidan marigayin da ke No. 60 Lamido Crescent a Kano don yi wa iyalinsa ta'ziyya.
KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa
Yana daga cikin yan siyasan da aka kafa jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP) tare da su a shekarar 1976 karkashin shugabancin marigayi malam Aminu Kano.
Ya kuma rike mukamin mataimakin shugaban Social Democratic Party (SDP) na kasa a yankin Arewa maso Yamma.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng