Dan Gwamna El-rufai ya wallafa hoton matan mahaifinsa, ya ce auren mata fiye da ɗaya yana da kyau

Dan Gwamna El-rufai ya wallafa hoton matan mahaifinsa, ya ce auren mata fiye da ɗaya yana da kyau

- Mohammed El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna, ya jinjinawa matan mahaifinsa a Twitter tare da wallafa hotonsu

- Bayanin mutumin da ya bayyana auren mata fiye da daya a matsayin abu mai kyau ya haddasa cece-kuce a kafar sadarwar ta zamani

- Sharhin ya rarrabu tsakanin waɗanda suke sha’awar abun da kuma mutanen da suka yi gargadi a kan shiga cikin lamarin tara mata

Dan Gwamna Nasir El-Rufai, Mohammed, a ranar Juma’a, 19 ga Fabrairu, ya saka hotunan matan mahaifinsa a Twitter.

Yaron ya yaba wa auren mata fiye da ɗaya a matsayin abu mai kyau. A cikin hoton, gwamnan ya tsaya a bayan matasan yana mai murmushi da annashuwa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara ya yi amai ya lashe bayan ya ce ba duka yan bindiga bane na banza

Dan Gwamna El-rufai ya gabatar da matan mahaifinsa, ya ce auren mata fiye da ɗaya yana da kyau
Dan Gwamna El-rufai ya gabatar da matan mahaifinsa, ya ce auren mata fiye da ɗaya yana da kyau Hoto: @B_ELRUFAI
Source: Twitter

Da yake wallafa hoton a kan manhajar mai alamar tsuntsun, Mohammed ya ce:

"Auren mace fiye da daya yana da kyau. Na gabatar da iyayena mata!"

Mutane da yawa sun yi sharhi kan wallafar, inda hoton ya samu ‘like’ kusan 4,000 a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli wallafar tasa a kasa:

Yayinda wasu suka yarda da sallamawarsa, wasu kuma sunyi akasin haka. Legit.ng ta tattaro wasu sharhi a kasa:

@Jefarrh ya ce:

"Yana da kyau idan attajiri ne ke yin sa. Kada ku yaudare talakawa don Allah!"

@76937d1b967c46d ya ce:

"Ee, akwai kyau ƙwarai da gaske."

@morogun1 ya ce:

"Wa ya gaya maka cewa auren mata fiye da daya yana da daɗi ba za ka iya karanta zuciyoyinsu ta fuskokinsu ba."

@Sekoniolalekan1 ya ce:

"Auren mace fiye da daya yana da kyau idan kana da kudi sannan kuma ka bi koyarwar Alqurani da Sunna."

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban tsaro ya bayyana inda yakin Najeriya na gaba zai gudana

A wani labari na daban, an kama wata dalibar makarantar sakandare dauke da bindiga kirar pistol na gargajiya da aka ce tana shirin harbin malaminta a makaranta.

Wani malami a Makarantar Gwamnatin Sakandare na Ikot Ewa a jihar Cross ya umurci dalibar da aske gashin kanta da ta rina zuwa wani launi amma hakan ya fusata ta.

Bayan hakan ne dalibar ta zo makaranta dauke da bindiga. Daga bisani an gayyaci sojoji zuwa makarantar bayan kama dalibar da bindiga kamar yadda aka wallafa hotunan a kafafen sada zumunta.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel