Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi
- An kama dalibar makarantar sakandare a jihar Cross River dauke da bindiga a makaranta
- Rahotanni sun ce dalibar ta tafi da bindigar makaranta ne da nufin ta harbi malamin da ya ce ta aske gashin kanta
- Daga bisani an gayyaci sojoji su zo makarantar domin su karbi bindigar tare da mika ta ga hukuma
An kama wata dalibar makarantar sakandare dauke da bindiga kirar pistol na gargajiya da aka ce tana shirin harbin malaminta a makaranta
Wani malami a Makarantar Gwamnatin Sakandare na Ikot Ewa a jihar Cross ya umurci dalibar da aske gashin kanta da ta rina zuwa wani launi amma hakan ya fusata ta ta.
DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
Bayan hakan ne dalibar ta zo makaranta dauke da bindiga.
Daga bisani an gayyaci sojoji zuwa makarantar bayan kama dalibar da bindiga kamar yadda aka wallafa hotunan a kafafen sada zumunta.
KU KARANTA: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng