PDP ta bukaci a sallami Ministan Tsaron Nigeria ba tare da ɓata lokaci ba

PDP ta bukaci a sallami Ministan Tsaron Nigeria ba tare da ɓata lokaci ba

- Jam'yyar PDP ta yi kira da cewa a kori Ministan Tsaro na Nigeria, Bashir Magashi daga aiki

- Jam'iyyar adawar ta yi wannan kiran ne biyo bayan kalaman ministan na cewa yan Nigeria su dena tsoron yan bindiga

- PDP ta ce wannan abin takaici ne da ke nuna ministan bai san aikinsa ba idan har zai ce mutane marasa makamai su kare kansu alhalin aikinsa ne ya kare su

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira da cewa a sallami Ministan Tsaro, Manjo janar Bashir Magashi daga aikinsa ba tare da bata lokaci ba saboda rashin yin aikinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Jam'iyyar cikin sanarwar da sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar ta ce ta bukacin hakan ne furucin da ya yi na cewa jama'ar Nigeria marasa makamai su kare kansu daga hare-haren yan bindiga da yan ta'adda.

PDP ta bukaci a sallami Ministan Tsaron Nigeria ba tare da ɓata lokaci ba
PDP ta bukaci a sallami Ministan Tsaron Nigeria ba tare da ɓata lokaci ba. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

A cewar sanarwar, "Jam'iyyar ta bayyana ministan a matsayin mai sakaci, wanda bai san aikinsa ba kuma tabbacin cewa gwamnatin Buhari ta yi wa bata gari saranda kuma bata da niyyar yakarsu.

"Bamu taba tunanin gwamnati za ta kira jama'an gari marasa makamai da yan bindiga da yan ta'adda ke kaiwa hari 'ragwaye' ba yayinda wadanda aka zaba su kare su suna zaune a ofisoshinsu a Abuja."

Sanarwar ta PDP ta ce irin wannan yunkurin kauce sauke nauyi na gwamna alama ne da ke tabbartwa cewa Nigeria na neman zama kasar da ta gaza a karkashin gwamnatin Buhari tunda gwamnati ba za ta iya aikinta ba na maganin yan bindiga da masu tada kayan baya.

KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

Babban jam'iyyar hammayar ta kuma koka kan abinda ta kira 'samar wa bata gari sana'a mai riba' saboda kudin fansa da ta ce a kan bawa masu garkuwa a maimakon a yake su.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel