2023: PDP tayi magana kan zargin tsayar da Atiku da kuma tsige shugabanta na kasa

2023: PDP tayi magana kan zargin tsayar da Atiku da kuma tsige shugabanta na kasa

- PDP ta ce har yanzu ba ta samu dan takarar shugaban kasa wanda zai daga tutar jam’iyyar a 2023 ba

- Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar, ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga ikirarin cewa tuni aka zabi Atiku a matsayin mai tutar

- Ologbondiyan ya kuma yi watsi da ikirarin cewa PDP na shirin korar shugabanta na kasa, Secondus

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi watsi da rahotannin kafafen yada labarai da ke ikirarin cewa tana shirin dawo da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa a 2023.

Kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya bayyana a ranar Laraba, 17 ga watan Fabrairu, cewa jam’iyyar ba ta da dan takarar shugaban kasa har yanzu tunda ba ta sayar da fom din tsayawa takara ga kowa ba, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Satar Kagara: Gwamnan Neja ya gana da Buhari, ya yi karin haske a kan ceto su

2023: PDP tayi magana kan zargin tsayar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa da tsige shugabanta
2023: PDP tayi magana kan zargin tsayar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa da tsige shugabanta Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ologbondiyan ya ce PDP a shirye take da ta kare dimokiradiyya a koyaushe kuma ba za ta taba goyon bayan tursasa wa mutane 'yan takara ba.

Ya ce:

“Ba mu fara sayar da fom ba, har sai zuwa wannan lokacin, ba mu san wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023 ba. Bugu da kari, ba mu fara sayar da fom dinta ba."

Hakazalika, kakakin na PDP ya ce jam'iyyar ba ta yin wani shiri na tsige shugabanta na kasa, Prince Uche Secondus, kamar yadda ake ikirarin a wasu wurare.

Ya sake nanata cewa jam’iyyar ta dunkule kuma tuni ta dukufa wajen karbe mulki daga hannun APC a 2023.

KU KARANTA KUMA: Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

A wani labari na daban, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai samu damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC ba a zaben shugaban kasa 2023.

Saraki ya bayyana hakan a ranar Talata bayan ya tasa 'yan kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP zuwa gidan tsohon shugaban kasar dake Abuja.

A taron da suka yi da Jonathan an samu labarai iri-iri na batun shugabannin jam'iyyar APC da tsohon shugaban kasar wanda ya janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani, inda har wasu suke zaton APC za ta tsayar da Jonathan takara a 2023.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng