Yanzu Yanzu: Tawagar manyan jami’an gwamnati sun isa garin Minna kan sace daliban Kagara

Yanzu Yanzu: Tawagar manyan jami’an gwamnati sun isa garin Minna kan sace daliban Kagara

- Tawagar gwamnatin tarayya da suka hada da shugabannin tsaro da ministoci sun isa Minna, jihar Neja

- Hakan ya biyo bayan sace daliban makarantar kimiya ta gwamnati da yan bindiga suka yi

- Lamarin ya afku ne a daren ranar Talata, 16 ga watan Fabrairu

Labari da muke samu ya nuna cewa a yanzu haka, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Mohammed Babagana Monguno, Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, suna a garin Minna, babban birnin jihar Neja..

Sauran tawagar sune ministan labarai, Lai Mohammed da takwaransa na harkokin yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi.

Wannan yana daga cikin kokarin da gwamnatin tarayya ke yin a ceto yaran kwalejin kimiya ta gwamnati, Kagara wanda yan bindiga suka sace a daren jiya Talata, 16 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Arewa ga mutanen Arewa: Kada ku kai wa ‘yan kudu hari a arewa

Yanzu Yanzu: Tawagar manyan jami’an gwamnati sun isa garin Minna kan sace daliban Kagara
Yanzu Yanzu: Tawagar manyan jami’an gwamnati sun isa garin Minna kan sace daliban Kagara
Asali: Getty Images

Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin sadarwa ta zamani, Bashir Ahmed ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa a Twitter:

A yanzu haka, babban mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Shugaban yan sandan Najeriya, ministan labarai da na harkokin yan sanda suna Minna daga cikin aikin ceton Gwamnatin tarayya na daliban kwalejin kimiyya ta gwamnati, Kagara, wanda yan fashi suka sace a daren jiya.”

A wani labarin, mun ji cewa a wani dan cikas da aka samu a kokarin da ake na magance matsalar rashin tsaro a kasar, wasu da ake zargin 'yan fashi ne sun sace matafiya da dama a jihar Neja.

An yi garkuwa da matafiyan ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairu, a kan wata babbar hanya, inda rahotanni suka nuna cewa masu garkuwar sun nemi a ba su kudi har Naira miliyan 500 kafin su sake su.

KU KARANTA KUMA: Malami ya shawarci FG da ta kirkiro hukumar kula da ayyukan makiyaya

Wata kungiyar yan ta’adda ta saki bidiyon matafiyan suna rokon gwamnati da ta kwato musu yanci a ranar Talata, 16 ga Fabrairu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel