Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri

Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri

- Mummunar gobara wacce ta yaye saman kwanon sansanin 'yan gudun hijira ta yi sanadiyyar mutuwar wani jariri

- Al'amarin ya faru ne a wani sansanin 'yan gudun hijira dake wurin titin Mafa a Maiduguri, jihar Borno a ranar Talata

- Ganau sun tabbatar da yadda jaririn ya babbake ta yadda ba za a gane shi ba yayin da wasu manya kuma suka kone a wasu wurare

Wata mummunar gobara ta yi ajalin wani jariri a wani sansanin 'yan gudun hijira dake wuraren titin Mafa a cikin Maiduguri jihar Borno a ranar Talata.

Ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da misalin 7:30am na safiya a wani bangare na sansanin amma an samu nasarar kashe gobarar cikin karamin lokaci.

A cewar ganau din: "Wata gobara ta barke da misalin 1pm kuma ta yi sanadiyyar kone tanti da dama dake sansanin."

Wani jariri ya kone kurmus sannan wasu manya biyu sun kone kamar yadda ganau din ya tabbatar.

KU KARANTA: UNN ta dakatar da malami, hukuma ta damke shi a kan dirkawa daliba ciki

Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri
Mummunar gobara ta barke, gidaje 620 sun kone na 'yan gudun hijira a Maiduguri. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

An gano cewa wurin kwanan mutane 620 ne ya kone sakamakon gobarar wacce 'yan kwana-kwana suka taru suka kashe, jaridar The Punch ta wallafa.

Mukaddashin shugaban NEMA na mazabar arewa maso gabas din Maiduguri, Ishaya Chinoko, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce Needs Assessment tare da BOSEMA da wasu gidauniyoyi na tallafa wa jama'a suna kokarin ganin sun gyara wurin da suka kone.

"Kwanan nan za a samar da wadanda wurarensu suka kone matsuguni," a cewarsa.

A gaba daya sansanin akwai mutane 14,250 ne suke zama daga kananun hukumomi 3, Dikwa, Mafa da kuma Bama, Kamar yadda shugaban yace.

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

A wani labari na daban, gwamnonin yankin arewa maso yamma a ranar Litinin sun sha alwashin yin amfani da duk wasu hanyoyin da za su iya wurin bai wa rayuka da kadarori kariya a yankin.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a Kaduna yayin wani taro da ofishin mai bai wa kasa shawara a fannin tsaro ya hada, Vanguard ta wallafa.

Masari wanda yayi jawabi a madadin dukkan takwarorinsa, ya ce tsaro a yankin ya tabarbare don haka dole ne gwamnonin su yi aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng