Zamu dage sosai wajen inganta tsaro a Arewa maso gabas, in ji Buhari

Zamu dage sosai wajen inganta tsaro a Arewa maso gabas, in ji Buhari

- Gwamnonin jihar Borno da Yobe sun yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Gwamnan jihar Borno ya bayyanawa manema labari dalilin zaman, ya kuma yabawa shugaban

- Shugaban kasa ya tabbatar da samar da abubuwan da suka dace don inganta tsaro a yankin

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ayyukan soji da ke gudana a yankin Arewa maso Gabas za su dore domin tabbatar da tsaron yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Babagana Zulum ya nakalto shugaban yana fadar haka ne bayan wata ganawar sirri da yayi da wata tawaga daga jihohin Borno da Yobe

Tawagar karkashin jagorancin gwamnoni Zulum da Mai Mala Buni na jihohin Borno da Yobe, sun hada da tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, da ministocin jiha na aikin gona, Mustapha Shehuri, da na ayyuka da gidaje, Abubakar Aliyu.

KU KARANTA: Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ondo

Zamu dage sosai da ayyukan sojoji a Arewa maso gabas, in ji Buhari
Zamu dage sosai da ayyukan sojoji a Arewa maso gabas, in ji Buhari Hoto: The Punch
Asali: UGC

Gwamnan jihar ta Borno wanda ya yiwa manema labarai bayanin fadar gwamnatin jihar kan sakamakon taron, ya ce tawagar ta bukaci shugaban kasar da ya kara yawan sojoji da jami’an tsaro a yankin na Arewa maso Gabas.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa shugaban kasan ya yarda da shawarin nasu.

“Ya zuwa yanzu, yana da kyau, Shugaban kasa ya amsa ga gwamnati da mutanen Borno da Yobe cewa zai yi duk abin da zai yiwu cikin wadatar kayan aiki don tabbatar da dorewar ayyukan soji da ke gudana a yankin." in ji gwaman jihar Borno.

KU KARANTA: EFCC: Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta yaba wa Buhari kan nadin Bawa

A wani labarin, Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci jami’an rundunar‘ yan sanda ta Najeriya da su jajirce tare da nuna rashin tausayi akan “masu aikata laifuka”, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar, da ke Abuja, yayin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro, wanda aka sanya wa suna “Operation Puff Adder II”, don karfafa yakin da ake yi da ‘yan fashi, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel