Idan Fani Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba shi ba, in ji jigon PDP

Idan Fani Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba shi ba, in ji jigon PDP

- Wani jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana cewa PDP zata ruguje matukar Kayode ya bar ta

- Jigon ya fadi haka ne a martaninsa ga fadin wani gwamna da yake sukar Kayode kan APC

- Jigon ya kuma bayyana kwarewar Kayode a fannin siyasa da ba abu ne mai sauki ba

Wani jigo a jam’iyyar PDP, kuma Shugaban kungiyar Revival na PDP, Malam Tanko Ibrahim ya caccaki tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose kan kalaman da ke cewa Idan Kayode ya bar PDP, zai mutu a siyasance.

Mallam Tanko Ibrahim ya fadi wannan bayanin ga jaridar Vanguard a ranar Talata.

Ku tuna a baya an ruwaito cewa Gov Fayose ya bayyana cewa ya tabbata dari bisa dari Fani-Kayode ba zai bar PDP ba, cewa idan har ya bar ta karshe zai mutu a siyasance a matsayinshi na sahun gaba dan Najeriya.

KU KARANTA: Kada ku tausayawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda

Idan Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba Kayode ba, in ji jigon PDP
Idan Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba Kayode ba, in ji jigon PDP Hoto: Africa Daily News
Source: UGC

Da yake mayar da martani game da sanarwar, Tanko, wani jigon PDP na arewa, ya ce Gov Fayose bai cika tabo kan matsayin Fani-Kayode a matsayin shugaban PDP ba.

“Gwamna Fayose ya rasa yadda za ayi da gaskiyar abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar, ta yaya za ka ce Fani-Kayode zai mutu a siyasance idan ya bar PDP?

"Fani-Kayode ya kasance kashin bayan jam’iyya mai mulki tun lokacin da gwamnatin Buhari ta hau mulki a 2015 ”

“Idan FFK ya bar PDP to PDP ce za ta mutu a siyasance ba FFK ba. Shi ne karfi da kwazo a bayan PDP. ”

“Shi ne wanda ke hana kowa a kasar da ke adawa da Buhari ya tafi da ruhin fadarsa. Ba tare da FFK ba, APC za ta ci PDP a karin kumallo. ”

KU KARANTA: Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ogun

A wani labarin, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nuna damuwarta kan rikicin kabilanci a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, wanda ya kai ga rasa rayukan mutane da dama, Vanguard News ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rashin fahimta tsakanin kabilun biyu daban-daban a kasuwar Shasa da ke karamar Hukumar Akinyele a Ibadan ta haifar da rikici na kabilanci wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel