EFCC: Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta yaba wa Buhari kan nadin Bawa
- Biyo bayan nadin sabon shugaban EFCC, wata kungiya ta yabawa shugaba Buhari
- Kungiyar ta siffanta nadin da cancanta da kuma bai wa ma'aikacin damar nuna kwarewarsa
- Hakazalika kungiyar ta bukaci majalisar dattawa su yi kyakkyawan bincike kan sabon shugaban
Wata kungiya a karkashin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa da mutunci ta yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nadin Mista Abdulrasheed Bawa, a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).
Ta hanyar nadin, Bawa mai shekaru 40 ya zama mafi karancin shekaru da ya shugabanci Hukumar, Vanguard News ta ruwaito.
Da yake maida martani kan nadin ta wata sanarwa dauke da sa hannun Shugaban kungiyar yaki da cin hanci da rashawa, Kwamared Prince Kpokpogri, ya bayyana zabar Bawa a matsayin mafi kyawun abin da ya faru a matakin shugabancin EFCC.
KU KARANTA: ‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya
"A gare mu a cikin kungiyoyin farar hula, muna farin ciki da Shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki Abdulrasheed Bawa a matsayin wanda ya dace ya shugabanci EFCC.
"Mun yi korafi sau da yawa cewa jami'i kwararre a cikin Hukumar ya kamata a ba shi dama. Muna godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ba mu kunnen saurare.
Taron, sun yi kira ga Majalisar Dattawa da ta yiwa sabon shugaban na EFCC kyakkyawan bincike.
“Wani sabon aiki ne a EFCC. Muna kira ga majalisar dattijai da ta ga Bawa ya cancanci wannan matsayin ta hanyar ba shi kyakkyawan bincike da tabbatarwa.
KU KARANTA: 'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace
A wani labarin, A ranar 16 ga watan Fubrairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC.
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu abubuwa da ya kamata a sani game da Mista Abdulrasheed Bawa.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng