'Yan bindiga sun kashe mutane 2, Bam ya raunata yara 7 a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutane 2, Bam ya raunata yara 7 a Kaduna

- Wasu 'yan bindiga dadi sun harbe wasu mutane a wasu yankunan jihar Kaduna a Najeriya

- Hakazalika wata fashewar wani abu ta jikkata yara bakwai a wani yankin na jihar Kaduna

Gwamnatin jihar ta koka kan lamarin, ta kuma mika sakon jimami da addu'ar neman sauki

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu a kananan hukumomin Kachia da Igabi na jihar Kaduna, yayin da yara bakwai suka samu raunuka sakamakon fashewar wani abu cikin hatsarin a Ungwan Mangoro, The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a Kaduna ya kara da cewa yaran da suka jikkata na karbar kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello, Shika.

A cewarsa, “A wani abin bakin ciki, hukumomin tsaro sun ba da rahoton cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Akwando da ke karamar hukumar Kachia, kuma sun kashe wani dattijo Dikko Bagudu, wani mazaunin yankin.

KU KARANTA: EFCC: Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta yaba wa Buhari kan nadin Bawa

'Yan bindiga sun kashe mutane 2, fashewar bam ya raunata yara 7 a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mutane 2, fashewar bam ya raunata yara 7 a Kaduna Hoto: TopNaija.ng
Source: UGC

“A wani lamarin kuma, 'yan fashi da makami sun tare hanyar Sabon Birni zuwa Rikau, karamar hukumar Igabi suka kashe wani mai suna Ibrahim Abdulmumin, wani mazaunin kauyen Rikau.

"Wani mai suna Sahabi Shafiu, ɗan shugaban ƙauyen Rikau, shi ma ya ji rauni. An bayar da rahoton cewa dukkan wadanda abin ya shafa suna dawowa daga kasuwar mako-mako da ke Sabon Birni lokacin da 'yan fashin suka kama su.

“Gwamna Nasir el-Rufai ya nuna bakin ciki game da rahotannin kuma ya yi ta’aziyya ga dangin mutanen biyu da aka kashe, yayin da ya ke yin addu’o’in neman juriya. Ya kuma yi fatan wadanda aka raunata a kauyen Rikau su samu sauki cikin gaggawa. ”

Da yake ci gaba da magana, Aruwan ya ce, “Hukumomin tsaro sun ba da rahoton fashewar wani abu ba zato ba tsammani a wani gida da ke Ungwan Mangworo, karamar hukumar Igabi.

KU KARANTA: Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ondo

A wani labarin, Masu garkuwan da suka sace wasu bakin da suka halarci bikin aure a jihar Delta sun bukaci iyalan wadanda abin ya shafa su biya N10m.

Jaridar PUNCH Metro ta tattaro daga majiyoyi na kusa da wadanda aka sacen cewa masu garkuwan sun bude tattaunawa da iyalansu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel