‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya

‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya

- Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya da aka fi sani da Shi'a sun bukaci adalci ga 'yan uwansu

- Kungiyar ta koka kan yadda gwamnati ke ci gaba da tsare mutanen kungiyar masu yawa

- Hakazalika, kungiyar ta kirayi gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin shugabanta

Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wanda aka fi sani da Shi'a, ta bukaci a yi wa mambobinta sama da dubu daya adalci a kan zargin kisan sojoji a Zariya, Jihar Kaduna, a ranar 15 ga Disamba, 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana wannan bukatar ne yayin kaddamar da wani littafi domin tunawa da lamarin kwanan nan, a Abuja.

Littafin, mai taken ‘December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria; Survivors Accounts’, Farfesa Isa Hassan Mshalgaru ne ya yi bitar shi.

KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya
‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya Hoto: DW
Asali: UGC

Ya ce dangane da abubuwan da aka bayyana a cikin littafin, amfani da kalmar kisan kiyashi ya bayyana yadda aka kashe dimbin fararen hula.

"Littafin ya ba da labari mai rikitarwa game da zaluncin sojoji a kan mambobin IMN," in ji shi.

Ya kara da cewa abin da ya faru a Zariya yana kan hanya daya tare da barayin Zaki Biam da Odi na 2001 da 1999.

Shima da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Babban Sakataren kungiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Dr. Ebenezer Oyetokun, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki shugaban kungiyar wanda yake tsare tun 2015.

KU KARANTA: PDP ta yi Allah-wadai game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

A wani labarin, Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci jami’an rundunar‘ yan sanda ta Najeriya da su jajirce tare da nuna rashin tausayi akan “masu aikata laifuka”, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar, da ke Abuja, yayin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro, wanda aka sanya wa suna “Operation Puff Adder II”, don karfafa yakin da ake yi da ‘yan fashi, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel