An yanke wa wanda ya kashe jami'in Jumia hukuncin kisa ta hanyar rataya

An yanke wa wanda ya kashe jami'in Jumia hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Wata kotu a jihar Ribas ta yankewa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya ko harbi

- Matashin an kamashi da laifin kashe wani jami'in Jumia bayan kawo masa wayar IPhone

- Alkalin ya bayyana matashin a matsayin mara imani, mara tausayi kuma mara nuna nadama

Mai shari’a Chigozie Igwe na babbar kotun jihar Ribas da ke zaune a Fatakwal ta yanke wa wanda ya kashe wakilin jigilar kasa na Jumia Chukwuma Eleje hukuncin kisa ko dai ta hanyar rataya ko kuma harbi da bindiga.

Sodienyem Mbatumukeke ya kashe Eleje, 37, a Fatakwal kimanin shekaru hudu da suka gabata lokacin da ya kawo wayar iphone a gidan Mbatumukeke, The Nation ta ruwaito.

Daga baya an gano gawarsa a cikin kwandon shara a cikin gidan.

KU KARANTA: ‘Yan Shi’a sun nemi ayi musu adalci kan kisan gilla da aka musu a Zariya

An yanke wa wanda ya kashe jami'in Jumia hukuncin kisa ta hanyar rataya
An yanke wa wanda ya kashe jami'in Jumia hukuncin kisa ta hanyar rataya Hoto: PM News
Asali: UGC

An gurfanar da Mbatumukeke da kuma wata Excel Destini a kan kisan jami'in.

Da take yanke hukunci a ranar Litinin, kotun ta sake tare da wanke Destiny amma ta samu Mbatumukeke da laifi dumu-dumu kamar yadda ake tuhumarsa.

Justice Igwe ya bayyana Mbatumukeke a matsayin mai taurin kai mai laifi wanda bai cancanci jin kai ba, ya kara da cewa bai yi nadama ba.

Ya ce, “An same ka da laifin kisan wakilin jigilar kaya na Jumia a ranar 25 ga Maris, 2017 kuma an yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.

"Za a ɗaure ka hannu biyu da ƙafa a rataye a wuyanka har ka mutu, ko kuma ta hanyar harbi da bindiga, zunubinka kuwa ya hau kanka.” Justice Igwe ya sanar.

KU KARANTA: Jihar Legas ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya, gwamna jihar

A wani labarin, Masu garkuwan da suka sace wasu bakin da suka halarci bikin aure a jihar Delta sun bukaci iyalan wadanda abin ya shafa su biya N10m.

Jaridar PUNCH Metro ta tattaro daga majiyoyi na kusa da wadanda aka sacen cewa masu garkuwan sun bude tattaunawa da iyalansu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel