Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da ‘Dan shekara 40 da zai jagoranci EFCC

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da ‘Dan shekara 40 da zai jagoranci EFCC

- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban EFCC

- Mr. Abdulrasheed Bawa zai gaji kujerar da Ibrahim Magu ya bari a 2020

- Bawa ya shafe shekaru fiye da 15 ya na aiki a matsayin jami’in hukumar

A ranar 16 ga watan Fubrairu, 2021, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC.

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu abubuwa da ya kamata a sani game da Mista Abdulrasheed Bawa, ainihin mutumin Jega, jihar Kebbi.

1. Mista Abdulrasheed Bawa zai iya zama shugaban EFCC ya na da shekara 40, mafi karancin shekarun wanda ya rike hukumar.

2. Abdulrasheed Bawa ya na cikin sahun farko na jami’an da aka koya wa aiki a lokacin da aka kafa hukumar EFCC a kasar.

KU KARANTA: Buhari ya zabi Bawa a matsayin shugaban EFCC

3. Sabon shugaban EFCC jami’i ne da ya yi shekara da shekaru ya na aikin binciko masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

4. Mista Bawa ya kware a harkar binciken manyan satar kudi, safarar makudan kudi, da satar kudi ta banki da sauran laifuffuka.

5. Jami’in ya samu horo a kasashen ketare bayan Digirin a fannin tattalin arziki, da digirgir a ilmin harkokin kasar waje a Jami'ar UDUS.

6. Sabon shugaban na EFCC ya yi kwas a harkar bankado marasa gaskiya, ya na da satifiket a bangaren CFE da kuma CAMS.

7. Bawa a lokacin ya na matsayin “Deputy chief detective superintendent”, ya rike babban ofishin hukumar EFCC na Fatakwal.

8. Bayan nan, Bawa ya rike shugaban babban ofishin EFCC na reshen Ibadan, ya jagoranci ayyukan hukumar a Kudu maso yamma.

Abubuwa X da ya kamata ka sani game da ‘Dan shekara 40 da zai jagoranci EFCC
Abdulrasheed Bawa da Shugaban kasa
Asali: UGC

KU KARANTA: IGP ya ba Jami'an 'Yan sanda umarni damko marasa gaskiya

9. An taba rahoto ana zarginsa da ba daidai ba a lokacin da ya ke kan kujerar shugaban EFCC na shiyyar Fatakwal a lokacin Ibrahim Magu.

10. Idan an tabbatar da Bawa a Majalisa, zai zama cikakken shugaban EFCC na farko da aka yi bayan Ibrahim Lamorde, wanda ya sauka a 2015.

A shekarar da ta wuce ne shugaban kasa ya tunbuke Ibrahim Magu daga kujerar shugaban EFCC.

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu.

EFCC ta zabi Mohammed Umar a matsayin shugaban rikon kwarya wanda ya rike kujerar zuwa yanzu.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng