Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu na wasu yan majalisa biyu

Yanzun nan: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu na wasu yan majalisa biyu

- Yar majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Otukpo / Ohimini ta Benue, Hon. Blessing Onuh, ta sauya sheka daga jam'iyyar APGA zuwa APC mai mulki

- Har ila yau, mamba mai wakiltar mazabar Bauchi a majalisar, Hon. Yakubu Abdullahi, shima ya sauya sheka daga PRP zuwa APC

- Su dukka biyun sun sauya sheka ne saboda rikicin da ya addabi jam'iyyunsu wanda a karkashinsu ne suka ci zabe

'Yar tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark kuma mamba mai wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini ta Benue, Hon. Blessing Onuh, ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga All Progressive Grand Alliance (APGA).

Mamba mai wakiltar mazabar Bauchi a majalisar, Hon. Yakubu Abdullahi, shima ya sauya sheka daga jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) zuwa APC, jaridar The Nation ta ruwaito.

A cikin wasiku biyu mabanbanta wanda kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya karanta, ‘yan majalisar biyu sun ce sun bar jam’iyyun da suka dauki nauyin zabukansu saboda rikicin da ake fama da shi a dukkan matakan jam’iyyun.

Yanzun nan: Yan majalisar dokokin tarayya 2 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
Yanzun nan: Yan majalisar dokokin tarayya 2 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC Hoto: @GuardianNigeria
Source: Twitter

Onuh ta ce ta bar APGA ne saboda rikicin shugabanci a dukkan matakan jam'iyyar, inda ta kara da cewa ta yanke shawarar ficewa ne bayan da ta tattauna da mutanen ta.

KU KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya: Gwamna Akeredolu ya roki Shugaba Buhari da ya yi jawabi ga ’yan Najeriya

Ta yabawa shugabancin jam'iyyar APC na kasa kan yadda suka bari sauya shekar ta yiwu.

A nashi bangaren, Abdullahi ya ce ya yanke shawarar barin PRP ne saboda rikici, wanda ya haifar da fitowar shugabannin jam’iyyar na kasa guda biyu da kuma shugabanni biyu a jihar Bauchi.

Ya ce Alhaji Falalu Bello da Farfesa Sule Bello suna ikirarin zama shugaban jam'iyyar tare da hedkwata biyu na kasa mabanbanta.

Ya kuma ce daya daga cikin bangarorin jam'iyyar a jihar Bauchi ya rubuta masa takardar dakatar da shi daga jam'iyyar.

Dan majalisar ya ce rikicin da ke faruwa a jam'iyyar na jihar Bauchi abun damuwa ne matukar saboda hakan ya haifar da takaddama tsakanin mambobin jam'iyyar.

KU KARANTA KUMA: Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel ya koma jam'iyyar All Progressive Congress, APC mai mulki, Vanguard ta ruwaito.

Gbenga jigo ne a babban jam'iyyar hamayya ta PDP kuma shine ya jagoranci yakin neman zaben shugabancin kasa na Atiku Abubakar.

Ana sa ran Daniel zai tafi ya karbi katin jam'iyarsa na APC kafin a rufe yin rajistan sabbin yan jam'iyyar a yau Talata.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel