Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare

Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare

- Gwamnatin jihar Binuwai ta rufe Kwalejin Vaatia da ke Makurdi saboda wata baƙuwar cuta

- Kwamishinan lafiya na jihar, Joseph Ngbea ne ya bayar da sanarwar a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairu

- Ngbea ya ce daliban makarantar biyar sun kamu da wannan baƙuwar rashin lafiyar

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ba da umarnin rufe wata makarantar sakandare, Kwalejin Vaatia, da ke Makurdi, babban birnin jihar, bayan barkewar wata baƙuwar cuta.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa bayan rufe makarantar, hukumar makarantar ta aika wata sanarwa ga iyaye da masu rikon yaran, a ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairu, kan su zo su dauki yaransu.

Legit.ng ta tattaro cewa daliban makarantar guda biyar sun kamu da wannan baƙuwar cuta kuma suna kwance a asibitin koyarwa da asibitin Madonna duk a Makurdi.

Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare
Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare Hoto: @GovSamuelOrtom
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe

Jaridar da ta ziyarci makarantar a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, ta ce an ga wasu iyaye suna kwasan yaransu.

Joseph Ngbea, kwamishinan lafiya na jihar, ya ce daliban makarantar biyar sun kamu da wannan rashin lafiyar.

Kwamishinan ya bayyana bakuwar rashin lafiyar a matsayin ‘Ciwon Orepa” yana mai cewa ɗaliban sun sami tabin hankali.

Ya ce daliban makarantar biyar sun kamu inda ya kara da cewa an rufe makarantar ne don gujema yaduwar cutar.

“Dalibai biyar lamarin ya shafa, uku a Asibitin Koyarwa sannan daya daga cikinsu na samun sauki yayin da wasu biyu ke asibitin Madonna (wani asibiti mai zaman kansa). Kun san cewa Najeriya na kan aiwatar da takardar shaidar rashin kwayar cutar shan inna, yanzu, mun ga cewa wasu daliban na fama da matsala. (ba cikakkiyar nakasa ba). Haƙiƙa suna samun sauki.

“Tunda babu cutar inna, an kawar da cutar shan inna kwata-kwata daga ciki. Don haka ana kiran ciwon da Orepa, muna kokarin duba hakan, ana basu kulawa, a yanzu, ba a gano cutar a asibitin koyarwa ba."

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali

Da aka tambaye shi ko cutar na iya yaduwa, kwamishinan ya ce:

“Wannan shine dalilin da yasa muka rufe makarantar, ilmin kwayar cutar, muna so mu bincike ta, tana yaduwa, shi yasa muka nemi a rufe makarantar. Gwamnatin Benue ta rufe makarantar sakandare saboda wata bakuwar cuta."

A wani labarin, Majalisar masu harhada magunguna a Najeriya ta ce jihohin Yobe da Zamfara dukkansu biyun na da kantunan magunguna guda 22 ga kuma karancin kwararrun likitocin magunguna.

Majalisar ta ce sabanin yadda mutane da yawa za su yi tunani, yawan matsalar rashin tsaro a Arewa ba shi da nasaba da halin da ake ciki.

Kwamitin PCN yayi magana game da binciken da aka buga a cikin Journal of Pharmaceutical Policy and Practice.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel