Rikicin makiyaya: Gwamna Akeredolu ya roki Shugaba Buhari da ya yi jawabi ga ’yan Najeriya

Rikicin makiyaya: Gwamna Akeredolu ya roki Shugaba Buhari da ya yi jawabi ga ’yan Najeriya

- Gwamna Rotimi Akeredolu ya nuna damuwar sa kan rikicin da makiyaya masu aikata laifuka ke haddasawa

- Gwamnan jihar Ondo ya yi kira ga gwamnatin Buhari da ta dauki kwakwaran mataki kan lamarin

- Akeredolu ya zargi makiyaya masu tayar da tarzoma da aikata wasu laifuka da ke faruwa a dazukan Ondo

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fito fili ya yi Allah wadai da ayyukan ta’addanci da miyagun makiyaya ke yi.

A cewar jaridar The Nation, Akeredolu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, a yayin wata hira a gidan talabijin na Channels TV.

KU KARANTA KUMA: Baƙuwar cuta ta bulla a Binuwai yayinda Ortom ya rufe makarantar sakandare

Rikicin makiyaya: Gwamna Akeredolu ya roki Shugaba Buhari da ya yi jawabi ga ’yan Najeriya
Rikicin makiyaya: Gwamna Akeredolu ya roki Shugaba Buhari da ya yi jawabi ga ’yan Najeriya Hoto: Femi Adesina/Facebook, @RotimiAkeredolu/Twitter
Source: UGC

Ya ce:

“Abin da muke tsammani daga Shugaban kasa shi ne ya fito ya sanar da’ yan Najeriya cewa shi ba ya goyon bayan aikata laifuka. Ya taba cewa, duk wadanda kuka samu da makamai ba tare da lasisi ba, to a kama su.''

Gwamnan ya roki hukumomin tsaro da su yi iya bakin kokarinsu wajen hana makiyaya aikata ayyukan ta’addanci.

Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta gano cewa wasu makiyaya na amfani da gandun daji a jihar don aikata laifuka.

Akeredolu ya kuma bayyana cewa Sunday Adeyemi wanda aka fi sani da Igboho, wanda ya jagoranci gwagwarmaya da makiyaya, ya zama fitacce ne saboda wasu lamura.

Ya yi kira da a binciki yanayin da ya sa Igboho tsoma baki a cikin al'amuran tsaro.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe

Gwamnan na Ondo ya bayyana cewa ba ya goyon bayan saba doka da mutanen da ke daukar doka a hannunsu, inda ya jadadda cewa shi ya sa ya ke kira ga mutanen da ke kudu maso yamma da su guji tashin hankali ko daukar doka a hannu.

A gefe guda, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tare da wasu gwamnonin Arewacin Najeriya yanzu haka suna kasuwar Shasha domin ganewa idanuwansu irin bannar da akayi yayinda rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Gwamnonin Arewan sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle; da gwamnan jihar Neja. Abubukar Sani Bello.

Gwamnonin sun dira jihar Oyo ne a daren Litinin domin ganawa da gwamnan jihar kan abinda ya faru ranar Juma'ar da ta gabata inda akayi asarar rayuka da dukiya.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel