Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe

- Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda da yawa a jihohin Yobe da Borno

- Hakazalika, Sojojin sun ce sun lalata sansanonin ‘yan ta’addan a yayin artabun

- Sai dai kuma, wani soja ya rasa ransa yayin da wasu hudu suka ji rauni a arangamar

A cikin wani lamari da zai faranta zuciyar 'yan Najeriya da dama, sojoji na Birgediya 21 da 26 na rundunar Sojojin Najeriya da ke samun goyon baya daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF sun kashe ‘yan ta'adda 81 a kauyuka biyar na Dajin Sambisa.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Madu Bukar, wani shugaban Civilian JTF da ke taimakawa sojoji wajen yakar ‘yan ta’addan ne ya tabbatar da hakan.

KU KARANTA KUMA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 81, sun rasa wani jami’insu a Borno da Yobe Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

An ruwaito shi yana cewa:

“Sojojinmu da ke cikin daji a wannan watan sun gamu da turjiya mai karfi daga‘ yan ta’adda, wadanda suka dasa abubuwan fashewa (IEDs) a hanyoyin da sojoji ke bi.

"Mun rusa sansanonin 'yan ta'addan tare da kwato motocinsu na bindiga da sauran makamai, yayin da suke tserewa daga kauyukan da aka kakkabe."

Da yake ci gaba da bayani, ya bayyana cewa wani soja ya rasa ransa a yakin yayin da hudu suka ji rauni sakamakon fashewar abubuwa.

Sojojin Birgediya 28 a karamar hukumar Chibok sun ragargaji mahara 31 a ranar Laraba, 10 ga watan Fabrairu, a garin Askira Uba da ke jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Ana saura makonni 3 auren sojan Najeriya, 'yan bindiga sun sheke shi har lahira

Sojojin sun kuma lalata motocin bindiga guda tara daga cikin sha daya da maharan suka yi amfani da su.

A wani labarin, mun ji cewa TVC ta ruwaito cewa dakarun Sojojin Najeriya yanzu haka suna artabu da yan ta'addan Boko Haram (ISWAP) a karamar hukumar Marte, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ta bayyana cewa Sojojin sun samu nasarar ceton mutanen da yan ta'addan suka sace amma har yanzu ba'a san adadin rayukan da aka rasa ba.

Marte na yammacin tafkin Chadi, inda rikicin Boko Haram yayi kamari.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel