Gwamnonin Arewa 4 sun kai ziyara Ibadan don ganin irin bannar da akayi

Gwamnonin Arewa 4 sun kai ziyara Ibadan don ganin irin bannar da akayi

- An yi asarar rayuka da dukiya a rikicin da ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Oyo

- Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da rikicin kabilan da ya auku a Ibadan

- Gwamnonin sun kai ziyaran ne don ganewa idanuwansu abinda ya faru

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, tare da wasu gwamnonin Arewacin Najeriya yanzu haka suna kasuwar Shasha domin ganewa idanuwansu irin bannar da akayi yayinda rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa.

Gwamnonin Arewan sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle; da gwamnan jihar Neja. Abubukar Sani Bello.

Gwamnonin sun dira jihar Oyo ne a daren Litinin domin ganawa da gwamnan jihar kan abinda ya faru ranar Juma'ar da ta gabata inda akayi asarar rayuka da dukiya.

Gwamna Makinde, ya yi alkawarin cewa za'a biya dukkan wadanda sukayi asaran wani abu diyya.

KU KARANTA: Jerin wadanda suka rike mukamin shugaban hukumar EFCC a tarihin Najeriya

Gwamnonin Arewa 4 sun kai ziyara Ibadan jihar don ganin irin bannar da akayi
Gwamnonin Arewa 4 sun kai ziyara Ibadan jihar don ganin irin bannar da akayi Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA NAN: Zargin ba shi mukami a DPR: Hadimin Buhari da hukumar sun magantu

Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya ba da umarnin tura rundunoni hudu na 'yan sandan kwantar da tarzoma don magance rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan jihar Oyo.

Shiga tsakani da rundunar kwantar da tarzomar sun hada da jami'an Ofishin Leken Asirin na kasa da kuma helikopta mai sa-ido guda daya daga sashen jigilar 'yan sanda.

Amma mai magana da yawun rundunar, CP Frank Mba, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai taken, ya ce jami'an za su karfafa tsaro da kuma karfafa gwiwar jama'a kan yankunan da rikicin ya shafa.

Source: Legit.ng

Online view pixel