Jihar Legas ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya, gwamna jihar

Jihar Legas ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya, gwamna jihar

- Gwamnatin jihar Legas ta bayyana yadda jihar ke ci gaba wajen kasuwancin jan nama

- Jihar ce ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya kamar yadda gwamnan ya fada

- Gwamnatin jihar ta yi kira ga sanya hannun jari mai yawa a fannin samar da jan nama

Rabin dukkan dabbobin da ake samarwa a Najeriya ana cinyesu su ne a Legas kadai, in ji gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bayyana hakan yayin kaddamar da sabon mayankar shanu da awaki a karkashin hadin gwiwar Gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu a Bariga.

Ya sanar da cewa jihar ta Legas tana da mahauta kusan 16 daga ciki goma sha daya mallakar. gwamnatin jiha.

KU KARANTA: PDP ta yi Allah-wadai game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

Jihar Legas ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya, gwamna jihar
Jihar Legas ke cinye 50% na dabbobin da ake kiwo a Najeriya, gwamna jihar Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Wannan a cewarsa bayyanannen nuni ne na yadda ƙananan sana'o'i zasu iya girma zuwa manyan. Ya ba da tabbacin jajircewar gwamnatinsa kan harkar noma, ya kara da cewa za a aiwatar da dukkan tsare-tsare a bangaren.

Gwamnan yayin da yake yabawa mai gudanarwa na mahautar, Alhaji Olayiwola Niniola saboda juya karamar mahautar ta zama ta zamani; ya yi kira ga karin masu saka hannun jari da su ba da tasu gudummawar a bangaren samar da jan nama a Jihar Legas.

Ya ce: “Wannan babban misali ne na ruhin 'damar-yi’ kuma dole ne in yaba wa Alhaji Niniola don sauya wannan wuri. Idan aka kalli yanayin yadda wannan mayankar take a shekarun da suka gabata, irin wannan abin kallo ne mara dadi amma yanzu, yana da kyau.”

Ita ma da take magana, Kwamishinar Aikin Gona ta Jihar Legas, Madam Abisola Olusanya, yayin da take jaddada bukatar samar da karin mahauta a jihar don biyan bukatun mutane, ta nemi karin zuba hannun jari na kashin kai a kasuwancin mahauta.

Da yake tsokaci kan bukatar inganta tsafta da kuma sayar da nama, kwamishinan ya yi gargadin cewa ba za a yarda da yankan ba bisa ka'ida ba a cikin jihar.

KU KARANTA: Kada ku tausayawa 'yan ta'adda, IGP ya fadawa rundunar 'yan sanda

A wani labarin, Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel