PDP ta yi Allah-wadai game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

PDP ta yi Allah-wadai game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

- Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da hare-haren juna dake faruwa a jihar Oyo

- Jam'iyyar ta nuna damuwarta kan hare-haren da cewa hakan abin kunya ne

- Ta kuma kirayi gwamnatin tarayya da ta maida hankali don magance rikicin

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta nuna damuwarta kan rikicin kabilanci a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, wanda ya kai ga rasa rayukan mutane da dama, Vanguard News ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rashin fahimta tsakanin kabilun biyu daban-daban a kasuwar Shasa da ke karamar Hukumar Akinyele a Ibadan ta haifar da rikici na kabilanci wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran ta na Kasa, Mista Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Litinin a Abuja, jam'iyyar ta bayyana rikicin a matsayin abin ban haushi kuma ta yi kira da a kwantar da hankali yayin da mahukunta suke bankado abin da ya haifar da zubar da jinin.

KU KARANTA: Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya

PDP ta nuna damuwar ta game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan
PDP ta nuna damuwar ta game da rikicin Hausawa da Yarbawa a Ibadan Hoto: The Africa Report.com
Source: UGC

Ologbondiyan ya yi tir da yadda rikicin kabilanci ya ta’azzara a sassa daban-daban na kasar nan, inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da mafita mai dorewa kan rikice-rikicen da ke faruwa a kasar.

Ya shawarci gwamnati da ta kawo cikakkiyar nauin doka a kan duk wani ko wata kungiya da aka samu da inganta rarrabuwar kai, rashin bin doka, rashin adalci da kuma keta haddin hannun gwamnatin tarayya.

Ologbondiyan, ya yabawa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo saboda matakan da ya dauka na dawo da zaman lafiya a jihar.

"Jam'iyyarmu tana jajantawa wadanda rikicin ya rutsa da su tare da yin kira ga dukkan mutane masu imani da su yi taro don tabbatar da zaman lafiya a kasarmu ta hanyar samar da adalci, bin doka da kuma mutunta hanyoyinmu na tarayya."

KU KARANTA: IGP ya tura rundunonin 'yan sandan kwantar da tarzoma Oyo

A wani labarin, Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel